Showing posts with label ‘kabilanci. Show all posts
Showing posts with label ‘kabilanci. Show all posts
Tuesday

Yadda gwamnan PDP ya jagorancin korar 'yan APC daga majalisar jiharsa.
'Yan majalisar na APC sun shiga zauran majalisar a safiyar yau inda su kayi wata zama cikin gaggawa kuma suka dakatar da wasu 'yan majalisar guda 11.
Nse Ntuen mai wakiltan mazabar Essien Udim a jihar na ya jagoranci zaman.
Sauran yan majalisar hudu sune, Gabriel Toby mai wakiltar mazabar Etim Ekpo/Ika; Otobong Ndem mai wakiltar Mkpat Enin; Victor Udofia mai wakiltar mazabar Ikon sai Idongesit Ituen mai wakilatan mazabar Itu.
Suna nan a cikin harabara majalisar a yayinda gwamnan jihar Udom Emmanuel wadda ke jam'iyyar PDP ya iso majalisar tare da jami'an tsaro da wasu matasa masu goyon bayan PDP kuma ya tarwatsa zaman da 'yan majalisar keyi.
An yi harbe harbe da kana an kone mota guda a hayaniyar da ta faru a majalisar a yau.
A baya. Legit.ng ta kawo muku cewa yan sanda sun sake rufe majalisar dokokin na jihar Akwa Ibom karo na biyu a cikin mako biyu.
An gano cewa yan majalisar jihar biyar da aka sallama kwana-kwanan nan ne suka kai hari majalisar tare da jami'an 'yan sanda da 'yan daba.
Rahoton ya bayyana cewa 'yan majalisar da aka sallama na dauke da sandar ikon majalisar kuma sun shirya tsige kakakin majalisar kana su dakatar da mambobi 21 na majalisar da kuma tsige gwamnan jihar.
Wannan na zuwa ne wasu 'yan kwanaki bayan shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki ya umurci yan sandan su bar harabar majalisar domin ya majalisar su shiga zaurensu su cigaba da ayyukansu.
SOURCE @LEGIT.NG
Nse Ntuen mai wakiltan mazabar Essien Udim a jihar na ya jagoranci zaman.
Sauran yan majalisar hudu sune, Gabriel Toby mai wakiltar mazabar Etim Ekpo/Ika; Otobong Ndem mai wakiltar Mkpat Enin; Victor Udofia mai wakiltar mazabar Ikon sai Idongesit Ituen mai wakilatan mazabar Itu.
Suna nan a cikin harabara majalisar a yayinda gwamnan jihar Udom Emmanuel wadda ke jam'iyyar PDP ya iso majalisar tare da jami'an tsaro da wasu matasa masu goyon bayan PDP kuma ya tarwatsa zaman da 'yan majalisar keyi.
An yi harbe harbe da kana an kone mota guda a hayaniyar da ta faru a majalisar a yau.
A baya. Legit.ng ta kawo muku cewa yan sanda sun sake rufe majalisar dokokin na jihar Akwa Ibom karo na biyu a cikin mako biyu.
An gano cewa yan majalisar jihar biyar da aka sallama kwana-kwanan nan ne suka kai hari majalisar tare da jami'an 'yan sanda da 'yan daba.
Rahoton ya bayyana cewa 'yan majalisar da aka sallama na dauke da sandar ikon majalisar kuma sun shirya tsige kakakin majalisar kana su dakatar da mambobi 21 na majalisar da kuma tsige gwamnan jihar.
Wannan na zuwa ne wasu 'yan kwanaki bayan shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki ya umurci yan sandan su bar harabar majalisar domin ya majalisar su shiga zaurensu su cigaba da ayyukansu.
SOURCE @LEGIT.NG
Abin Da Amurka Tace Game Da Kisan Kiyashi A Jos.
Kasar Amurka tayi magana game da rikicin da ke aukuwa a tsakiyar Najeriya inda ta nemi a dauki mataki. Kwanan nan ne wani rikici ya barke a Garin Barkin Ladi da ke cikin Jihar Filato.
Heather Nauert wanda wani babban Jami’i ne a Gwamnatin Kasar Amurka ya fitar da jawabi game da kashe-kashen da ya auku kwanan nan. Gwamnatin na Amurka tace dole a hukunta wadanda su ka aikata wannan danyen aiki.
Hare-haren dai da aka kai sam ba su yi wa Gwamnatin Amurka dadi ba inda tayi kira da babban murya tana mai sukar lamarin da ake ta fama da shi a Arewacin Kasar. Amurka ta kuma yi wa al’ummar Yankin na Filato jaje.
Amurka ta nuna damuwan ta game da harin da ake kai wa a Yankin Arewa-maso-tsakiyan Najeriya da wasu sassa na Kasar. Kasar ta kuma yi kira ga Shugabanni su yi bakin kokarin na ganin kawo zaman lafiya a fadin Najeriya.
Nauert wanda shi ne ya fitar da wannan jawabi dai ya taya Shugaban Kasa Buhari takaicin abin da ya faru a Kasar sa. Shugaban Kasar dai tuni yayi Allah-wadai da wannan ta’adi ya kuma yi alkawarin magance matsalar.
Buhari Ya Jajantawa Al'ummar Filato : Bayan Asarar Rayuka Da Ya Faru A Garin
Jaridar Premium Time ta kasar nan ta bi diddikin abin da ya faru har ta kai rikici ya barke tsakanin Fulani da ‘Yan kabilar Birom a Garin Barkin Ladi da ke cikin Jihar Filato a karshen makon jiya.
Bincike ya nuna cewa kafin Ranar Asabar din da aka yi wannan kashe-kashe an hallaka wasu Fulani har 4 yayin da su ke dawowa daga wata kasuwar kara ta dabbobi a Garin Bukuru. Hakan ne ya jawo wasu Fulani su ka tashi su ka dauki fansa.
Wani Shugaban Fulani na Kungiyar su ta Miyetti Allah da ke Yankin Danladi Ciroma ya tabbatar da cewa ‘Yan kabilar Birom din sun kona mutanen su kurmus da ran su sannan kuma sun yi gaba da shanu sama da 300 na Fulanin da ke Yankin kafin nan.
Bayan wannan abin takaici ya faru ne wasu Fulani su ka shirya su ka kai wa ‘Yan Birom din hari. Su kuma dai ‘Yan kabilar Birom din sun yi ramuwar gayya daga baya inda su ka rika tare mutane a hanya su na kashe duk wadanda ba Mabiya addinin Kirista ba.
KARANTA WANNAN : Abin da Amurka tace game da kisan kiyashi a Jo's.
Daga cikin Fulanin da aka kashe akwai Bala Adamu, Isa Mohammed, Ibrahim Ahmed da Lawal Abubakar Dangana. A jiya dama kun ji cewa Jami’an tsaro dai sun tabbatar da cewa rikicin yayi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 86 a tashi guda a Jihar.
Saturday

Full Video : - Ankashe Musulmai Sama Da 4000 A Burma Rohingya Myanmar
InnãlillAhi Wa'inna IlaiHi Rãji'un.
HasbunallaHu wani'imal wakil.
Ya Allah ka isarwa musulunci da musulmai.
jama'a Wannan videon Kisan Gilla ne da Ake yima Musulmai kabilar Rohingya.
An maida Kisan Musulmi Yadda Kasan Kisan Kiyashi, Wannan Daukan Alhakai Haka Dame Yayi Kama?
Dan Allah Mallam Ka Daure Kayi Share&Download Na Wannan Videon Da Ake Kashe Musulman Wannan Kasa Ta “Burma”
A hakan Kuma Wai Gwamnati Tasan Da Wananna Kisan Gillar Da Ake yiwa wannan Al'uma Kuma Ta Kasa Daukar Mataki.
A Karshen Wannan Videon Zaku ga Wanda Ya Wallafa Videon Zuwa Ga Duniya Tasheda aki daya.
Wannan videon dai mun sameshi daga shafin pressloaded su kuma daga Dw hausa. Download Video below and Watch:-
DOWNLOAD VIDEO NOW
Friday

Yadda Jonathan yaci amanar musulunci A shekarar 2014
A ranar 31-December-2014 akayi taro
da ya shafi tsaro na "United Nations
Security Council" wanda shugaba
Buhari yakeyin irinsa a yau Talata 19-
September-2017.
Wancan taron, an tsara za'ayi kuri'ane
tsakanin kasashe 15 da ake kira "15-
member security council".
Wannan kuri'a kuwa za'ayi ta ne domin tabbatar da wasu abubuwa kamar haka: da
farko dai, kasar Musulmai ta Palestine
wacce kasar Yahudawan Israel ke
zalumta, an fitar mata da wasu
abubuwa kamar haka--wanda kuma
dukkan kasashen larabawa suka yarda
akai--cewar, za'a samu watanni 12
domin tsagaita wuta na rikici tsakanin
Palestine da Israel, a cikin watanni 12
nan, za'a fara shirye-shirye don
tabbatar da halastacciyar kasar
Palestine harma da basu East
Jerusalem a matsayin babbar helkwata
na kasarsu, sannan a cikin wadannan
watannin dukkan sojojin kasar Isreal da
suka mamaye yankunan Palestine za su
fita su janye dakarunsu, duka cikin
watanni 12 din can har zuwa wa'adi na
karshe a shekarar 2017 din nan, daga
nan ba za'a sake ganin sojojin Isreal a
kasar Palestine ba balle su yi ta kashe
yara da matansu da zalumtar
musulman Palestine, sannan har yanzu
kuma, da tabbatar da cewar yan gudun
hijira na Palestine da suke kasar Israel
su ma za'a basu damar komawa
gidajensu lafiya kalau. Wadannan
dukansu na cikin abinda waccar kuri'a
za ta tabbatar.
Ga yadda aka tsara abin, idan Palestine
ta samu kuri'ar kasashe 9 cikin 15 suka
goyi baya, to za'a tabbatarwa da
Palestine wadancan muradun nata
duka, daga nan za su fita cikin takura,
zalunci, da ketare iyaka irinnan
Yahudawan Israel.
Nigeria ta kasance a koda yaushe tana
goyon bayan duk wani abu da ya shafi
Palestine, don haka ma ake ganin
cewar Nigeria za ta shiga sahun masu
goyon baya a wancan karon.
Ana haka, sai Palestine ta samu goyon
bayan kasashe 8 dukansu sun mara
mata baya, sun hada da, China, France,
Russia, Argentina, Chad, Chile, Jordan
da kuma Luxemburg. Nigeria ce ta 9
wajen kada kuri'a, don haka yan
Palestine sun fara murna domin ganin
irin yadda Nigeria ke goya musu baya.
Ana haka sai ga jakadan Nigeria a
wajen jefa kuri'ar, Prof. Joy Ogwu, ga
mamakin kowa sai kawai ya goyi bayan
kasashen Britain, Lithuania da kuma
Republic of Korea da Rwanda wajen
nuna rashin amincewa, Australia da
United States su ma suka nuna rashin
amincewarsu, shikenan wancan kudirin
ya bi iska. Yanzu Palasdinawa za su ci
gaba da bauta wa Yahudawan Isra'ila,
za'a ci gaba da yiwa matansu fyade,
kashe yaransu kanana, rushe gidajensu,
da kuma tabbatar da su a matsayin
"haramtacciyar kasa".
Bayan wannan zaben, sai ga Prime
Minister na kasar Israel, Benjamin
Netanyahu na cewa: "Ina mika godiyata
ga Amurka da Australia sannan da
godiya ta musamman ga shugaban
kaasar Rwanda, abokina Paul Kagame,
da kuma shugaban kasar Nigeria,
abokina Goodluck Jonathan".
Da aka tambaye shi yaya akayi Isra'ila
ta ci nasara, sai yace: "Na yi magana
da su biyun (Kagame da Jonathan)
kuma suka min alkawarin cewar ba za
su goyi bayan wannan kudurin ba, kuma
sun ciki alkawarinsu". Inji Netanyahu.
Shi kuma jakadan Palestine a Nigeria,
Montaser Abuzaid cewa yayi: "kasarsa
da mutanensa sun ji matukar bakin ciki
da mamaki ta yadda Nigeria ta juya
musu baya. Muna girmama Nigeria
sosai saboda Nigeria na daya daga
cikin kasashen farko da suka tabbatar
da halastacciyar kasar Palatine tun
shekarar 1988, kuma ta kasance tana
goyon bayanmu tun wancan lokacin,
amma abinda ta mana jiya ya kadamu".
Sannan ya sake cewar, sai da ya kira
Ministan Harkokin Waje na Nigeria ya
tambayeshi ko za su goyi bayansu, ya
tabbatar masa da cewar za su goyi
bayansu, anyi haka jiya kawai sai ya
wayi gari yau wai ya ji Nigeria ta juya
musu baya.
Daman an zargi Goodluck Jonathan
ganin cewar a "UN General Assembly"
an ganshi ya ware da Prime Minister na
Israel, Benjamin Netanyahu, Secretary
of State na Amurka Hillary Clinton,
Minster na tsaron kasar Israel Ehud
Barak, wanda ake ganin zamansu ne ya
chanja alkiblar Nigeria akan
Palasdinawa.
Yau gashi yan'uwanmu Palasdinawa
suna cikin halinda suke ciki na tashin
hankali, rashin tsaro, rashin zaman
lafiya da muzgunawa a dalilin hukuncin
mutum daya: Goodluck Jonathan. Yau
Palasdinawa za su iya cewar suna
halinda suke cikine a dalilin Nigeria,
tunda a wancan lokacin Nigeria ta samu
damar chanja alkiblarsu.
ALLAH YA ISA TSAKANINMU DA
JONATHAN, ALLAH KA YI MANA
MAGANINSA KA MASA ABINDA YA
MANA.
Wannan labarin na fassara ma'anarsa
ne daga littafin siyasar nan na Olusegun
Adeniyi mai suna "AGAINST THE RUN
OF PLAY -- how an incumbent
president was defeated".
Daga shafuka na 166-168. Shi ya kawo labarin, da kuma wasu labarun sosai akan siyasar Nigeria da kuma abubuwan da suka
faru a lokacin Jonathan irin wadannan
da kuma irinsu Boko Haram, Chibok da
abubuwa da yawa.
Thursday

Yadda sojoji suka ci uwar yaran Nnamdi kanu
Yadda Sojojin Nigeria suka suburbudi yaran Nnamdi kanu masu Fafutukar kafa yankinnan na biyafara.
Hoto: yayin da sojojin ke horasu.
A cikin wannan videon zaku ga yadda sojojin suka lakada musu duka kuma suka tilasta musu shija wani ruwa mai uban datti sukace musu suyi barci aciki hakanne yayi sanadiyyar mutuwar wasu a waje zakuga gawarwakinsu, yayin da wasu kuma suka jikkata suna a kwakkwance, gani dai akace ya koriji sai ku sauke wannan videon a wayoyinku kuga yadda abin ya faru.
Sai ku danna download buttun a nan kasa don saukewa.

Ko Kasan Cewa Kabilar Igbo nada Alakar jini tsakanin su da yahudawan israela (karanta)
Kimanin watanni 5 da suka wuce, NAIJ.com ta bada rahotan cewa wasu masu binciken kimiya na kasar Israela sun ziyarci garin Nnewi da ke jihar Anambra domin gudanar da bincike akan ikirarin cewa asalin yan kabilar ibo daga can israela suke, toh yanzu masu binciken sun dawo.
Har ila yau, NAIJ.com ta taba kawo rahoton ziyarar da masu binciken kimiyan israila suka kai zuwa asibitin tsohon direkta kuma shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Dr Dozie Ikedife duk dai saboda suyi bincike akan sinadarin gina rayuwa na 'DNA' a turance Deoxyribonucleic Acid da ka iya nuna musu idan akwai alaqa ta jini tsakanin kabilar ibo da mutanen israela.

Toh, yanzu dai masu binciken kimiyan sun
dawo garin Nnewi da sakamakon binciken da
sukayi akan sinadarin na DNA da zai
warware wannan muqaballar. Masu binciken
kimiyan sun taho ne karkashin jagorancin
shugaban wata kungiya mai suna Jewish
voice ministries.
Wannan ziyarar tasu itace na hudu zuwa
garin Nnewi din domin kawo sakamakon
binciken da sukayi wanda rahotanni suka ce tabbas mutanen kabilar ibo da ke kudu maso gabashin Najeriya suna da alaqa da mutanen kasar Israela.

Rahotanni sun ce shugaban rikon kwaryar
kwamitin Nnewi ta arewa, Prince Chukwudi
Orizu ne ya tarbe su a Messianic Faith
Assembly a Uruagu.
WATCH THE VIDEO
Subscribe to:
Posts (Atom)




