Kasar Amurka tayi magana game da rikicin da ke aukuwa a tsakiyar Najeriya inda ta nemi a dauki mataki. Kwanan nan ne wani rikici ya barke a Garin Barkin Ladi da ke cikin Jihar Filato.
Heather Nauert wanda wani babban Jami’i ne a Gwamnatin Kasar Amurka ya fitar da jawabi game da kashe-kashen da ya auku kwanan nan. Gwamnatin na Amurka tace dole a hukunta wadanda su ka aikata wannan danyen aiki.
Hare-haren dai da aka kai sam ba su yi wa Gwamnatin Amurka dadi ba inda tayi kira da babban murya tana mai sukar lamarin da ake ta fama da shi a Arewacin Kasar. Amurka ta kuma yi wa al’ummar Yankin na Filato jaje.
Amurka ta nuna damuwan ta game da harin da ake kai wa a Yankin Arewa-maso-tsakiyan Najeriya da wasu sassa na Kasar. Kasar ta kuma yi kira ga Shugabanni su yi bakin kokarin na ganin kawo zaman lafiya a fadin Najeriya.
Nauert wanda shi ne ya fitar da wannan jawabi dai ya taya Shugaban Kasa Buhari takaicin abin da ya faru a Kasar sa. Shugaban Kasar dai tuni yayi Allah-wadai da wannan ta’adi ya kuma yi alkawarin magance matsalar.
No comments:
Write Comments