Thursday

Home Ko Kasan Cewa Kabilar Igbo nada Alakar jini tsakanin su da yahudawan israela (karanta)

Kimanin watanni 5 da suka wuce, NAIJ.com ta bada rahotan cewa wasu masu binciken kimiya na kasar Israela sun ziyarci garin Nnewi da ke jihar Anambra domin gudanar da bincike akan ikirarin cewa asalin yan kabilar ibo daga can israela suke, toh yanzu masu binciken sun dawo.

Har ila yau, NAIJ.com ta taba kawo rahoton ziyarar da masu binciken kimiyan israila suka kai zuwa asibitin tsohon direkta kuma shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Dr Dozie Ikedife duk dai saboda suyi bincike akan sinadarin gina rayuwa na 'DNA' a turance Deoxyribonucleic Acid da ka iya nuna musu idan akwai alaqa ta jini tsakanin kabilar ibo da mutanen israela.

Toh, yanzu dai masu binciken kimiyan sun
dawo garin Nnewi da sakamakon binciken da
sukayi akan sinadarin na DNA da zai
warware wannan muqaballar. Masu binciken
kimiyan sun taho ne karkashin jagorancin
shugaban wata kungiya mai suna Jewish
voice ministries.
Wannan ziyarar tasu itace na hudu zuwa
garin Nnewi din domin kawo sakamakon
binciken da sukayi wanda rahotanni suka ce tabbas mutanen kabilar ibo da ke kudu maso gabashin Najeriya suna da alaqa da mutanen kasar Israela.

Rahotanni sun ce shugaban rikon kwaryar
kwamitin Nnewi ta arewa, Prince Chukwudi
Orizu ne ya tarbe su a Messianic Faith
Assembly a Uruagu.

WATCH THE VIDEO
No comments:
Write Comments