Showing posts with label HIKAYOYI. Show all posts
Showing posts with label HIKAYOYI. Show all posts

Thursday

HIKAYAR BIRNIN DUWATSU 07

Na ci gaba da tarairayar su ina kara musu kwarin gwiwa a kasuwancinsu. Suka zama kullum suna bude rumfunansa da safe har zuwa yamma, yayin nan sai su rufe su dawo gidana mu ci abinci da abin sha tare, sa'annan mu kwanta. Ban taba bari suka taba kudinsu ba, komai suke so ni ke yi musu cikin kudina. Amma duk lokacin da muka zauna hira, babu zancen da suke yi sai na su dai suna son zuwa fatauci, zama wuri daya ya ishe su. Sai su yi ta ba ni labarin irin dukiyar da ake samu a fatauci, suka yi ta lallashina wai mu tafi tare in gani da idona. Suka ce wai muddin na dandana dadin da ke ga fatauci ba zan kara yarda na zauna gida ba kamar mace.



CIGABA.....




Abdullahi ya dubi karnuka ya tambaye su, "Haka aka yi, ya 'yan uwana?" Suka sunkuyar da kawunansu kasa, suka lumshe idanu, domin gasgata abin da ya fada. Sai ya ci gaba da labari ya ce, ya Shugaban Muminai, haka suka yi ta kwadaita mini romon fatauci har dai suka fara jan ra'ayina. Wata rana muna hira sai na ce musu, "Kai mu dai shirya mu tafi fataucin nan da kuke ta kwadaita mini, na ga abin da ake samu a ciki." Daga nan sai muka shiga shirin zuwa fatauci, muka kulla yarjejeniya a tsakaninmu. Muka sayi haja mai yawa muka sami jirgin fatake da zai tashi daga Basara muka sanya kayanmu. Jirgi ya mika cikin bahar mai yawan hauhawa, muka yi wa Basara adaboMuka sayi haja mai yawa muka sami jirgin fatake da zai tashi daga Basara muka sanya kayanmu. Jirgi ya mika cikin bahar mai yawan hauhawa, muka yi wa Basara adabo. Ba mu gushe ba muna keta ruwa har muka iso ga wani birni na daga cikin birane. Muka saya muka sayar, muka sami riba mai yawa. Muka kulle kayanmu daga wannan birni muka nufi wani. Haka muka yi ta bin birane da garuruwa da kauyuka muna ciniki muna samun riba, har muka sami dukiya mai yawa. Wata rana sai muka iso ga wani tsibiri na falalen dutse a tsakiyar teku. Madugu ya tsayar da jirgi a bakin dutsen ya ce mana, "Ya fatake, ku sauka cikin wannan tsibiri ku mike kafafunku, sa'annan ku binciko mana ruwan sha, domin namu ya yi nisa." Dukkan fatake suka sauka, har da ni, muka watsu bisa tsibirin dutse muna neman ruwa. Ni kuwa sai na haye bisa ko uwar dutsen ina dube-dube. Ba zato ba tsammani sai na ga wadansu macizai biyu, daya babba ne, bakikirin da shi, mummuna, ya biyo karamin wanda yake fari ne kyakkyawa har jikinsa na sheki kamardanyar azurfa. Da babban majcijin ya cimma karamin, sai na ga ya nannade shi kamar masu shirin barbara. Sai na ji karamin ya yi kara mai karfi cike da tausayi. Daga nan sai zuciyata ta raya mini watakila babban macijin nan so yake ya keta haddin karamin ya yi masa fyade. Don haka sai na suntumi wani katon dutse na dubi kan babban macijin nan na kwantara masa, nan take sai ga kwanya warwatse ko'ina. Ko kafin a yi haka, sai na ga karamin majicin nan ya juye siffa ya koma yarinya ma'abuciyar kyawo, da cikar halitta, da kwarjini, da haiba, da daidaito, ka ce ita wata ne mai haske yayin cikarsa. Ta zo gare ni ta kama hannuwana ta sumbata tana cewa, "Allah ya yi maka sutura da sutura biyu; sutura ta tsiraici a duniya, da sutura daga shiga wutar lahira ranar babbar tsayuwa, ranar da dukiya ba ta amfani walau 'ya'ya, face wanda ya je ga Allah da tsarkakakkiyar zuciya." Maciyar nan ta ci gaba da cewa, "Ya kai mutum, kai ka suturce mutuncina, ba zan manta da wannan alheri da ka yi mini ba harabada, idan Allah ya so zan saka maka da abin da ka yi mini." Tana gama fadin haka sai ta yi nuni da hannunta zuwa ga kasa, ta kece, ta shiga ciki, kasa ta game bisa gare ta. Ina ganin haka na gane cewa aljana ce. Macijin nan kuwa da na fashe wa kai sai wuta ta kama shi, ya cinye kurmus sai toka. Na yi mamakin wannan abu da na gani. Na koma ga abokan tafiyata na labarta musu abin da na gani, muka kwana cikin wannan tsibiri. Da gari ya waye, madugu ya kwance jirgi muka duru cikinsa. Aka tsayar da tutocin jirgi wadanda iska ke turawa, muka tafi cikin teku, tun muna hangen tsibirin nan har ya bace daga ganinmu. Muka yi ta keta ruwa tsawon kwana ashirin ba mu tarar da tudu ba, kai ko alamun tsuntsu ba mu gani ba balle mu sa rai akwai tsibiri ko gari kusa, har dan ruwan da muke sha ya kare. Da madugu ya ga haka sai ya ce mana, "Ya ku fatake, ruwanmu fa ya kare." Sai muka ce masa, to ya karkata jirgi zuwa ga kasa. Ya ce mana,

@hausapost28

"Wallahi ban san tafarkin da za ya kai mu ga tudu ba." Sai hankulanmu suka tashi, bakin ciki ya kama mu. Muka yi ta kuka muna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya shirye mu zuwa ga tafarki. Muka kwana ga wannan dare cikin mugun hali. Yayin da gari ya waye, ya haskaka da annurinsa, sai muka hangi wani dogon dutse a gabanmu. Da muka ga wannan dutse fa, sai muka shiga murna. Muna zuwa kusa gare shi sai madugu ya ce, "Ya ku fatake, ku sauka bisa wannan dutse ku nemo ruwan sha." Dukkanmu muka sauka, muka bazama neman ruwa amma ko tarfe ba mu samu ba, daga nan sai bakin cikinmu ya dawo danye. Na hau bisa ga birbishin dutse, na duba nesa gare mu, sai na hango wata da'ira, nisanta daga inda nake, tafiyar sa'a guda ko fiye. Na kira abokaina suka gabato, na ce da su, "Ku duba wancan kewaye na daga bayan dutsi, ni na ga birni matsawaicin gini, madaukakin sassa, ma'abucin soraye da katangu, da jigayi da kwaruruwa. Babu shakka za mu sami ruwa a cikinsa da sauran alheri. Mu tafi wannan birni mu zo da ruwa,mu kuma sayi abin bukatarmu a cikinsa, na daga waina da nama da abubuwan marmari." Sai suka amsa mini, "Mu muna jin tsoro, watakila mutanen wancan birni kafirai ne masu tsafi, su kama mu su bautar, ko ma su kashe mu, mu zama mun kai kanmu ga halaka da gangan. Ko ba ka ji yadda wani mai hikima yake cewa ba: 'Tun da aka halicci kasa take kasa, tun da aka halicci sama take sama. Wanda duk ya tashi daga kasa ya ce zai tafi sama, abin duk da ya same shi, shi ya jawo wa kansa.' Don haka mu ba za mu kai kanmu ga halaka ba." Na dube su na ce, "Ya ku fatake, hakika ba ni da iko a kanku. Amma zan dauki 'yan uwana mu tafi tare." 'Yan uwan nan nawa na jin haka sai suka ja da baya suka ce, "Mu ma muna jin tsoron abin da fatake suka ce, don haka ba za mu yi shahadar kuda ba." Na ce musu, "Ni kam tun da na yi alwashin zuwa sai na tafi, mai rabon ganin badi ko ana dakawa a turmi sai ya gani. Na dogara ga Allah da Ma'aikinsa. Ko za ku jira ni nan, na tafi na komo?"Abdullahi ya ce wa fatake, "Ko za ku jira ni nan, na tafi na komo?" Ya ci gaba da labari ya ce, yayin nan na bar su, na tafi har na isa kofar wannan birni. Na ga birni mai kyau da kyawun gine-gine, da al'ajabin zane, da madaukakan soraye, da tagogi adantattu, da dogayen katangu, gambunansu na karfen Siniya. Kofofinsu adantattu, zanannu masu dimautar da hankulla. Yayin da na shiga daga cikin birnin nan sai na ishe dandamali na dutse, a bisansa da wani mutum zaune da sarka ta bakin karfe daure ga damtsensa. A jikin sarkar akwai mabudai goma sha hudu. Da ganin haka sai na gane wannan mutum Sarkin Kofa ne, kuma birnin na da kofofi goma sha hudu. Na matsa kusa gare shi na ce, "Assalmu alaikum." Ya yi shiru, bai mayar mini da sallama ba. Na sake yi masa sallama ta biyu da ta uku, ya dai yi shiru bai ce mini 'ci kanka' ba. Na kara matsawa dab da shi, na aza hannuna bisa kafadarsa na ce, "Kai namiji, don me na yi maka sallama ba ka amsa mini ba. Shin kai kurma ne, ko barci kake yi, ko kai baMusulmi ba ne?" Bai amsa mini ba, kuma bai motsa ba. Da na lura da kyau sai na ga ashe dutse ne aka sassaka surar dan Adam, aka sanya masa sutura. Idan ka gan shi sai ka rantse da abin da zai kashe ka mutum ne mai rai. Na bar shi nan, na kutsa kai cikin birni, sai na ga mutane a kan hanya. Na tafi kusa ga daya, sai na ga shi ma dutse ne. Duk inda na shiga cikin birnin sai na tarar da mutane amma dukkansu na duwatsu. Na ga wata tsohuwa da tufafi da yawa bisa kanta, za ta wurin wanki, ita ma dutse ce, tufafin da ke kanta ma dutse ne. Na nufi kasuwa, na iske wani mutum mai sayar da mai, da ma'auni a hannunsa. A cikin rumfarsa ga kayan abinci iri iri, amma dukkansu dutse ne. Na ga mutane daban-daban, maza da mata, yara da manya, wasu zaune cikin rumfuna ana ciniki, wasu a tsaye, wasu suna tafiya, amma dukkansu duwatsu. Na yi mamaki gayar mamaki. Duk lokacin da na dauki wani abu na rike ga hannuna, sai ya roshe, ya zama kura. Can sai na ga wasu akwatuna na duwatsu, na bude daya,sai ga zinariya cunkus cikin jaka, da na taba jakar sai ta zama kura, amma zinariyar ba ta canja ba. Na damki zinariyar nan na cika aljifaina, na ce a raina, "Ina ma 'yan uwana sun biyo ni, da sun debi abin da suke iya diba na wannan zinariya da babu mai ita." Na shiga wata rumfar, ita ma na tarar da zinariya, amma babu inda zan saka ta, na cika aljifaina, na runguma ga habar riga, iyakar abin da zan iya runguma. Na bar wannan kasuwa na tafi ga wata, da na gama zagayawa cikinta ina kallon abin mamaki, na fita zuwa ga wata kasuwar. Haka na yi ta zagaya kasuwanninsu ina ganin abin al'ajabi, hatta karnuka da kyanwowinsu duka duwatsu ne. Na shiga kasuwar makera, na ga mutane zaune cikin rumfunansu, kowanne ya tasa hajarsa a gaba yana sayarwa, wasu da lu'ulu'u, wasu da jauhari. Yayin da na ga haka, ya Halifa, sai na watsar da zinariyar da na debo, na shiga dibar kayan makeran har na debi iya karfina. Na fita daga kasuwar makera ya zuwa ga kasuwar awon jauhari.

KU CIGABA DA KASANCEWA TARE DA MU A KODA YAUSHE

http://hausapost28.blogspot.com

Wednesday

HIKAYAR BIRNIN DUWATSU 06

. Sai su yi ta ba ni labarin irin dukiyar da ake samu a fatauci, suka yi ta lallashina wai mu tafi tare in gani da idona. Suka ce wai muddin na dandana dadin da ke ga fatauci ba zan kara yarda na zauna gida ba kamar mace.



CIGABA


Abdullahi ya dubi karnuka ya tambaye su, "Haka aka yi, ya 'yan uwana?" Suka sunkuyar da kawunansu kasa, suka lumshe idanu, domin gasgata abin da ya fada. Sai ya ci gaba da labari ya ce, ya Shugaban Muminai, haka suka yi ta kwadaita mini romon fatauci har dai suka fara jan ra'ayina. Wata rana muna hira sai na ce musu, "Kai mu dai shirya mu tafi fataucin nan da kuke ta kwadaita mini, na ga abin da ake samu a ciki." Daga nan sai muka shiga shirin zuwa fatauci, muka kulla yarjejeniya a tsakaninmu. Muka sayi haja mai yawa muka sami jirgin fatake da zai tashi daga Basara muka sanya kayanmu. Jirgi ya mika cikin bahar mai yawan hauhawa, muka yi wa Basara adaboMuka sayi haja mai yawa muka sami jirgin fatake da zai tashi daga Basara muka sanya kayanmu. Jirgi ya mika cikin bahar mai yawan hauhawa, muka yi wa Basara adabo. Ba mu gushe ba muna keta ruwa har muka iso ga wani birni na daga cikin birane. Muka saya muka sayar, muka sami riba mai yawa. Muka kulle kayanmu daga wannan birni muka nufi wani. Haka muka yi ta bin birane da garuruwa da kauyuka muna ciniki muna samun riba, har muka sami dukiya mai yawa. Wata rana sai muka iso ga wani tsibiri na falalen dutse a tsakiyar teku. Madugu ya tsayar da jirgi a bakin dutsen ya ce mana, "Ya fatake, ku sauka cikin wannan tsibiri ku mike kafafunku, sa'annan ku binciko mana ruwan sha, domin namu ya yi nisa." Dukkan fatake suka sauka, har da ni, muka watsu bisa tsibirin dutse muna neman ruwa. Ni kuwa sai na haye bisa ko uwar dutsen ina dube-dube. Ba zato ba tsammani sai na ga wadansu macizai biyu, daya babba ne, bakikirin da shi, mummuna, ya biyo karamin Wanda yake fari ne kyakkyawa har jikinsa na sheki kamardanyar azurfa. Da babban majcijin ya cimma karamin, sai na ga ya nannade shi kamar masu shirin barbara. Sai na ji karamin ya yi kara mai karfi cike da tausayi. Daga nan sai zuciyata ta raya mini watakila babban macijin nan so yake ya keta haddin karamin ya yi masa fyade. Don haka sai na suntumi wani katon dutse na dubi kan babban macijin nan na kwantara masa, nan take sai ga kwanya warwatse ko'ina. Ko kafin a yi haka, sai na ga karamin majicin nan ya juye siffa ya koma yarinya ma'abuciyar kyawo, da cikar halitta, da kwarjini, da haiba, da daidaito, ka ce ita wata ne mai haske yayin cikarsa. Ta zo gare ni ta kama hannuwana ta sumbata tana cewa, "Allah ya yi maka sutura da sutura biyu; sutura ta tsiraici a duniya, da sutura daga shiga wutar lahira ranar babbar tsayuwa, ranar da dukiya ba ta amfani walau 'ya'ya, face wanda ya je ga Allah da tsarkakakkiyar zuciya." Maciyar nan ta ci gaba da cewa, "Ya kai mutum, kai ka suturce mutuncina, ba zan manta da wannan alheri da ka yi mini ba harabada, idan Allah ya so zan saka maka da abin da ka yi mini." Tana gama fadin haka sai ta yi nuni da hannunta zuwa ga kasa, ta kece, ta shiga ciki, kasa ta game bisa gare ta. Ina ganin haka na gane cewa aljana ce. Macijin nan kuwa da na fashe wa kai sai wuta ta kama shi, ya cinye kurmus sai toka. Na yi mamakin wannan abu da na gani. Na koma ga abokan tafiyata na labarta musu abin da na gani, muka kwana cikin wannan tsibiri. Da gari ya waye, madugu ya kwance jirgi muka duru cikinsa. Aka tsayar da tutocin jirgi wadanda iska ke turawa, muka tafi cikin teku, tun muna hangen tsibirin nan har ya bace daga ganinmu. Muka yi ta keta ruwa tsawon kwana ashirin ba mu tarar da tudu ba, kai ko alamun tsuntsu ba mu gani ba balle mu sa rai akwai tsibiri ko gari kusa, har dan ruwan da muke sha ya kare. Da madugu ya ga haka sai ya ce mana, "Ya ku fatake, ruwanmu fa ya kare." Sai muka ce masa, to ya karkata jirgi zuwa ga kasa. Ya ce mana,

"Wallahi ban san tafarkin da za ya kai mu ga tudu ba." Sai hankulanmu suka tashi, bakin ciki ya kama mu. Muka yi ta kuka muna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya shirye mu zuwa ga tafarki. Muka kwana ga wannan dare cikin mugun hali. Yayin da gari ya waye, ya haskaka da annurinsa, sai muka hangi wani dogon dutse a gabanmu. Da muka ga wannan dutse fa, sai muka shiga murna. Muna zuwa kusa gare shi sai madugu ya ce, "Ya ku fatake, ku sauka bisa wannan dutse ku nemo ruwan sha." Dukkanmu muka sauka, muka bazama neman ruwa amma ko tarfe ba mu samu ba, daga nan sai bakin cikinmu ya dawo danye. Na hau bisa ga birbishin dutse, na duba nesa gare mu, sai na hango wata da'ira, nisanta daga inda nake, tafiyar sa'a guda ko fiye. Na kira abokaina suka gabato, na ce da su, "Ku duba wancan kewaye na daga bayan dutsi, ni na ga birni matsawaicin gini, madaukakin sassa, ma'abucin soraye da katangu, da jigayi da kwaruruwa. Babu shakka za mu sami ruwa a cikinsa da sauran alheri. Mu tafi wannan birni mu zo da ruwa,mu kuma sayi abin bukatarmu a cikinsa, na daga waina da nama da abubuwan marmari." Sai suka amsa mini, "Mu muna jin tsoro, watakila mutanen wancan birni kafirai ne masu tsafi, su kama mu su bautar, ko ma su kashe mu, mu zama mun kai kanmu ga halaka da gangan. Ko ba ka ji yadda wani mai hikima yake cewa ba: 'Tun da aka halicci kasa take kasa, tun da aka halicci sama take sama. Wanda duk ya tashi daga kasa ya ce zai tafi sama, abin duk da ya same shi, shi ya jawo wa kansa.' Don haka mu ba za mu kai kanmu ga halaka ba." Na dube su na ce, "Ya ku fatake, hakika ba ni da iko a kanku. Amma zan dauki 'yan uwana mu tafi tare." 'Yan uwan nan nawa na jin haka sai suka ja da baya suka ce, "Mu ma muna jin tsoron abin da fatake suka ce, don haka ba za mu yi shahadar kuda ba." Na ce musu, "Ni kam tun da na yi alwashin zuwa sai na tafi, mai rabon ganin badi ko ana dakawa a turmi sai ya gani. Na dogara ga Allah da Ma'aikinsa. Ko za ku jira ni nan, na tafi na komo?"Abdullahi ya ce wa fatake, "Ko za ku jira ni nan, na tafi na komo?" Ya ci gaba da labari ya ce, yayin nan na bar su, na tafi har na isa kofar wannan birni. Na ga birni mai kyau da kyawun gine-gine, da al'ajabin zane, da madaukakan soraye, da tagogi adantattu, da dogayen katangu, gambunansu na karfen Siniya. Kofofinsu adantattu, zanannu masu dimautar da hankulla. Yayin da na shiga daga cikin birnin nan sai na ishe dandamali na dutse, a bisansa da wani mutum zaune da sarka ta bakin karfe daure ga damtsensa. A jikin sarkar akwai mabudai goma sha hudu. Da ganin haka sai na gane wannan mutum Sarkin Kofa ne, kuma birnin na da kofofi goma sha hudu. Na matsa kusa gare shi na ce, "Assalmu alaikum." Ya yi shiru, bai mayar mini da sallama ba. Na sake yi masa sallama ta biyu da ta uku, ya dai yi shiru bai ce mini 'ci kanka' ba. Na kara matsawa dab da shi, na aza hannuna bisa kafadarsa na ce, "Kai namiji, don me na yi maka sallama ba ka amsa mini ba. Shin kai kurma ne, ko barci kake yi, ko kai baMusulmi ba ne?" Bai amsa mini ba, kuma bai motsa ba. Da na lura da kyau sai na ga ashe dutse ne aka sassaka surar dan Adam, aka sanya masa sutura. Idan ka gan shi sai ka rantse da abin da zai kashe ka mutum ne mai rai. Na bar shi nan, na kutsa kai cikin birni, sai na ga mutane a kan hanya. Na tafi kusa ga daya, sai na ga shi ma dutse ne. Duk inda na shiga cikin birnin sai na tarar da mutane amma dukkansu na duwatsu. Na ga wata tsohuwa da tufafi da yawa bisa kanta, za ta wurin wanki, ita ma dutse ce, tufafin da ke kanta ma dutse ne. Na nufi kasuwa, na iske wani mutum mai sayar da mai, da ma'auni a hannunsa. A cikin rumfarsa ga kayan abinci iri iri, amma dukkansu dutse ne. Na ga mutane daban-daban, maza da mata, yara da manya, wasu zaune cikin rumfuna ana ciniki, wasu a tsaye, wasu suna tafiya, amma dukkansu duwatsu. Na yi mamaki gayar mamaki. Duk lokacin da na dauki wani abu na rike ga hannuna, sai ya roshe, ya zama kura. Can sai na ga wasu akwatuna na duwatsu, na bude daya,sai ga zinariya cunkus cikin jaka, da na taba jakar sai ta zama kura, amma zinariyar ba ta canja ba. Na damki zinariyar nan na cika aljifaina, na ce a raina, "Ina ma 'yan uwana sun biyo ni, da sun debi abin da suke iya diba na wannan zinariya da babu mai ita." Na shiga wata rumfar, ita ma na tarar da zinariya, amma babu inda zan saka ta, na cika aljifaina, na runguma ga habar riga, iyakar abin da zan iya runguma. Na bar wannan kasuwa na tafi ga wata, da na gama zagayawa cikinta ina kallon abin mamaki, na fita zuwa ga wata kasuwar. Haka na yi ta zagaya kasuwanninsu ina ganin abin al'ajabi, hatta karnuka da kyanwowinsu duka duwatsu ne. Na shiga kasuwar makera, na ga mutane zaune cikin rumfunansu, kowanne ya tasa hajarsa a gaba yana sayarwa, wasu da lu'ulu'u, wasu da jauhari. Yayin da na ga haka, ya Halifa, sai na watsar da zinariyar da na debo, na shiga dibar kayan makeran har na debi iya karfina. Na fita daga kasuwar makera ya zuwa ga kasuwar awon jauhari.

KU CIGABA DA KASANCEWA DA MU

Monday

HIKAYAR BIRNIN DUWATSU 05

Wane kinibibi zai sa mu ce muna bin mahaifinka bashi, don dai son abin duniya. Dukkanmu mun san cewa cin dukiyar marayu babban laifi ne. Allah ya ji kan mahaifinka da rahama, ba mu san mai bin sa bashi ba, shi ne ma ke biyar mutane da yawa. Mahaifinka ba abin da ya ke gudu irin cin bashi, sau da yawa mukan ji shi yana addu'a, 'Allah ka tsare da cin bashi, Allah ka da ka dauki raina da bashin mutane ga wuyana.' Dukkanmu shaidu ne, idan ya dauki bashin mutum, nan da nan yake biyansa ba tare da mai kayan ya matsa masa ba. Idan kuwa kayansa aka dauka bashi, to ba ya takura wa wanda ya amshi kayan, idan ma talaka ne sosai sai ya yafe masa. Idan kuma ba talaka ba ne kuma mutumin ya mutu bai biya shi ba sai ya ce, 'na yafe masa,

CIGABA.......

Allah ya yafe masa laifukansa.' Don haka muna da tabbacin babu mai bin sa komai." Yayin da na ji haka sai na ce musu, "Na gode, Allah ya yi muku albarka." Daga nan sai na juya wurin wadannan 'yan uwa nawa na ce musu, "To kun ji, babu mai bin mahaifinmu bashi. Kun dai sani ya bar mana kudi masu yawa da gida da rumfa cike da kaya. Tun da mu uku ne, ke nan za a kasa dukiyar kashi uku kowa ya dauki kashi guda. Me kuka gani yanzu? Mu bar dukiyar yadda take muna juya ta tare, mu ci mu sha tare, ko kuwa a raba kowa ya dauki rabonsa ya shiga juyawa da kansa?" Suka ce mini, "Mun fi so a raba kowa ya dauki kasonsa." Abdullahi dan Falilu ya dubi karnuka ya ce, "Haka aka yi, ya 'yan uwana?" Suka sunkuyar da kai kasa suka lumshe ido, suna ishara da cewa, "Haka ne." Abdullahi ya ci gaba da labari ya ce, sai na kira wakilin alkali, ya Shugaban Muminai, ya raba mana dukkan dukiyar da mahaifinmu ya bari da kudi. Gida da rumfa suka fada cikin rabona, saboda 'yan uwana sun ce sun fi son tsabar kudi.Dukkanmu muka amince da wannan rabo, 'yan uwana suka kwashi kudi cunkus, ni kuwa aka bar mini gida da rumfa da 'yan kudi kadan, wadanda na sayi kayayyaki na zuba cikin rumfar, na zauna ina saye ina sayarwa. Amma 'yan uwana sai suka sayi haja mai yawa, suka dauki ijarar jirgin ruwa suka nufi wurin fatauci cikin duniya nesa da garinmu. Na yi musu addu'a, 'Allah ka yi musu budi, ni kam na fi so in zauna gida lafiya. Tsiya da kwanciyar hankali ya fi arziki da tashin hankali.' Na zauna tsawon shekara guda cikin rumfata, tswaon wannan lokaci kuwa Allah ya bude mini kofofin arziki, na sami riba ninkin-ba-ninkin, na tara dukiya kamar yadda mahaifinmu ya bar mana. Wata rana da hunturu, ana zazzaga sanyi, ina zaune cikin rumfata, na sanya riguna biyu, na gashi mai taushi, masu tamanin gaske, sai ga 'yan uwana sun zo gare ni. Kowane daga cikinsu na sanye da tsummar riga, duk ta kekkece har ana ganin fatar jikinsu. Ga lebbansu sun yi fari fat sun bushe, jikinsu sai makyarkyata yake yi saboda sanyin da ke bugun su...
www.shulaman.wapka.me
Wata rana da hunturu, ana zazzaga sanyi, ina zaune cikin rumfata, na sanya riguna biyu, na gashi mai taushi, masu tamanin gaske, sai ga 'yan uwana sun zo gare ni. Kowane daga cikinsu na sanye da tsummar riga, duk ta kekkece har ana ganin fatar jikinsu. Ga lebbansu sun yi fari fat sun bushe, jikinsu sai makyarkyata yake yi saboda sanyin da ke bugun su. Yayin da na gan su cikin wannan hali sai hankalina ya tashi, nan take tausayinsu ya kama ni. Na mike da sauri na rungume su ina hawaye. Na cire rigunan da na sanya na gashi na sanya wa kowannensu. Na ja su zuwa gidan wanka, na aika musu da tufafi masu tsada irin na tajirai, kowace tufa, tamaninta dinari dubu. Bayan sun yi wanka sun sanya tufafin da na ba su, sai na tafi da su zuwa gidana, na dauko kabakin abinci na girke musu, domin na lura da suna cikin matsananciyar yunwa. Na zauna muka ci abinci tare ina debe musu kewa da labarai na nishadi. Abdullahi ya juya ga karnuka ya tambaye su, "Haka aka yi, ya 'yan uwana?"Suka sunkuyar da kawunansu kasa suna lumshe idanu, suna cewa da ishara, "Haka ne!" Abdullahi ya ci gaba, yayin da suka ci suka koshi, ya Halifan Allah, sai na tambaye su, "Me ya faru gare ku? Ina dukiyarku?" Suka amsa mini, "Bayan mun yi cikon haja sai muka dauki jirgi muka fada cikin kogin Dujillati muka yi ta tafiya har muka iso ga wani gari mai suna Kufa, inda muka rika sayar da hajarmu da riba mai yawa, duk abin muka saye rabin dinari sai mu sayar da shi dinari goma, abin dinari guda kuwa muka sayar da shi dinari ashirin. Muka sami riba mai yawa wadda ba mu san iyakarta ba. Da muka sayar da hajar mu duka sai muka sayi haja irin ta Farisa. Abin da ake sayar wa a nan Basara dinari arba'in, a can sai muka saye shi dinari goma, da niyyar idan muka dawo nan mu ci riba daga gare shi. Daga Kufa muka shiga jirgi sai wani gari da ake kira Karhi, a nan ma muka saye muka sayar, muka sami riba mai dimbin yawa." Haka suka ci gaba da gaya mini garuruwan da suka tafi da irin ribar da suka samu. Saina tambaye su, "To, tun da kun sami irin wannan sa'ar fatauci, ya aka yi na gan ku cikin halin da kuka dawo?" Suka yi ajiyar zuciya, suka ce, "Ya dan uwanmu, muna tsammani wani mai kandun baka ne ya yi mana baki, ka san mutane ba su iya ganin abu su yi kurum. Bayan mun sami dukiya mai yawa daga wannan fatauci sai muka yi nufin dawowa gida. Muka sami babban jirgi muka sanya kayanmu, muka yi wa Basara tsinke. Muka kwana uku muna tafiya, a rana ta hudu sai bahar ta canja mana fuska. Ta tashi da hauka, tana toroko tana raurawa, iska mai karfi na kada ruwa, tozaye na tashi suna marin juna da wata irin kara kamar aradu da tartsatsi kamar na wuta a cikin duhun dare. Iska ta karkatar da jirginmu daga barin tafarki, ta kwashe shi ta fyada ga wani dutse da ya taso saman ruwa. Jirgi ya tarwatse dukkan dukiyarmu ta dulmiye cikin ruwa, muka yi ta kokarin ceton rayukanmu tsawon kwana daya da yini guda. Daga nan sai Allah ya koro mana da wani jirgi, matukansa suka taimake mu. Da muka sami kanmu sai mukanufo Basara, muna tafe muna bara daga wannan gari zuwa wancan. Muka sayar da tufafin jikinmu muka ci abinci, mun sha bakar wahala, wadda ba ta misaltuwa, a kan hanya kafin mu iso nan. Da a ce Allah ya nufa mun dawo da dukiyar da muka samu gida, to da ba za a sami mai kamarta ba duk garin nan, sai fa Sarki. Sai dai abin da Allah ya hukunta zai sami bawansa, to babu mai ikon ije shi." Na ce musu, "Ya 'yan uwana, kada wannan abu ya dame ku, ku gode wa Allah da ya tsirar da rayukanku. Idan da rai ai bawa ba ya yanke kauna. Wa ya sani ko a nan gaba ku sami wata dukiyar fiye da wadda kuka samu a baya." Na ci gaba da cewa, "Ya 'yan uwana, ku kaddara cewa kamar yau ne mahaifinmu ya mutu, wannan dukiya da ke hannuna tasa ce. Ina so mu sake raba ta daidai kamar yadda aka yi a baya." Na kira wakilin alkali na ce masa ya raba mana dukiyar nan a tsakaninmu. Ya kuwa raba mana ita kashi uku daidai, kowa ya dauki kashi guda. Na ce musu, "Ya 'yan uwana, Allah shi ne mai arzutta bawa a kowane gari yake.Kowane dayanku ya bude rumfa a cikin kasuwa ya zauna cikinta, watakila wannan ya zama silar arzikinku domin Allah shi ne masanin gaibi." Na taimaka musu suka bude rumfuna, suka saisayi kayayyaki suka zuba a ciki. Na ce musu, "Ku saya ku sayar, ku rika boye ribar kada ku barnatar, dukkan abin da kuke bukata na abinci da nama da abin sha, to ku yi mini magana zan ba ku." Na ci gaba da tarairayar su ina kara musu kwarin gwiwa a kasuwancinsu. Suka zama kullum suna bude rumfunansa da safe har zuwa yamma, yayin nan sai su rufe su dawo gidana mu ci abinci da abin sha tare, sa'annan mu kwanta. Ban taba bari suka taba kudinsu ba, komai suke so ni ke yi musu cikin kudina. Amma duk lokacin da muka zauna hira, babu zancen da suke yi sai na su dai suna son zuwa fatauci, zama wuri daya ya ishe su. Sai su yi ta ba ni labarin irin dukiyar da ake samu a fatauci, suka yi ta lallashina wai mu tafi tare in gani da idona. Suka ce wai muddin na dandana dadin da ke ga fatauci ba zan kara yarda na zauna gida ba kamar mace.

KU CIGABA DA KASANCEWA DA MU

Sunday

HIKAYAR BIRNIN DUWATASU 04

Halifa ya yi murmushi ya ce, "Idan na aika wani zai iya musantawa ya ce, 'ni ba ni da wasu karnuka,' amma idan kai ka tafi ka ce masa, 'na gan su da idona' ba shi da ikon musantawa. Don haka dole kai za ka tafi ka zo mini da shi da karnukan nan, idan kuwa ba haka ba ina yanka ka." Abu Is'haka ya ce, "Na ji, na dauka, ya Sarkin Musulmi, Allah ya agaje mu. Da ma an ce harshe shi ke yanka wuya. Laifina ne da na gaya maka wannan labari, amma ina so ka rubuta mini takarda da hannunka wadda zan ba shi."

CIGABA....


Halifa ya rubuta takarda ya ba shi, ya karba ya kama hanyar Basara. Yayin da Sarkin Basara ya ga ya komo nan da nan, sai ya ce, "Allah ya sa dai lafiya ka koma haka da wurwuri, ya Abu Is'haka? Ko harajin ne ya yi kadan Halifa ya ki karba?" Abu Is'haka ya dube shi cikin jin kunya ya ce, "Ya Sarki Abdullahi, harajinku ya cika daidai, Halifa ya karba cikin farin ciki. Amma ka gafarce ni saboda na ci amanar bakunta, wannan kuwa sharrin Shaidan ne!" Abdullahi ya tambaye shi cikin mamaki, "Wace amana ka ci tamu?" "Ka sani kwana uku da na yi tare da kai, a cikin kowane dare nakan bi bayanka, ba tare da ka sani ba, har zuwa dakin da kake bugun wasu karnuka biyu. Wannan al'amari ya sa ni mamaki matukar mamaki, ni kuma sai na ji kunyar na tambaye ka. Yayin da na koma Bagadaza sai kaikayin baki ya ja ni, na gaya wa Halifa wannan labari. Da na san zai nemi na dawo na tafi da kai tare da karnukan da ban gaya masa labarin ba, to amma kaddara ta riga fata, babu wanda ya isa ya canja kaddarar Ubangiji.Ga takarda Halifa ya ce a ba ka, a ciki yana umurtarka da ka tafi gare shi tare da karnukan nan. Amma don Allah ka yafe mini wannan laifi da na aikata maka." Ya duka ya yi ta ba shi hakuri. Abdullahi ya yi jugum yana tunani, can sai ya ce, "Babu komai da yake kai Halifa ya turo ba zan iya karyata ka ba, domin kai abokina ne. Amma da a ce wani ne ba kai ba, ya fada wa Halifa wannan labari, da na musanta wannan al'amari, na ce wa Halifa karya yake yi, ni ba ni da wasu karnuka. Amma yanzu zan dauki karnukan mu tafi tare ko da hakan zai zama karshen rayuwata." Abu Is'haka ya kama hannun Abdullahi ya sumbata yana cewa, "Allah ya rufa maka asiri kamar yadda ka rufa mini asiri ba ka karyata ni ga Halifa ba." Abdullahi ya shirya tsaraba mai kauri da zai kai wa Halifa, ya dauki karnuka tare da shi, ya aza kowanne bisa rakumi ya daure shi da sarkar zinariya, ya tafi tare da Abu Is'haka har suka isa Bagadaza gaban Halifa. Abdullahi ya dauki kasa a gaban Shugaban Muminai, ya umurce shi ya zauna.Da ya zauna sai ya jawo karnukan nan biyu gaban Haruna Rashid, wanda ya tambaye shi, "Mene ne labarin wadannan karnuka, ya Sarki Abdullahi?" Karnuka kuwa sai sumbatar kasa suke yi gaban Halifa suna kada wutsiya kamar masu kawo kara gare shi. Halifa ya cika da mamaki, ya dubi Abdullahi ya ce, "Gaya mini labarin wadannan karnuka da abin da ya sa kake bugun su kowane dare, sa'annan kuma ka ba su abinci kana rarrashi." Abudllah ya dukar da kansa kasa a gaban Halifa ya ce, "Ya Halifan Allah, wadannan ba karnuka ba ne face samari biyu, ma'abuta kyawu da cikar halitta da kwarjini da daidaito. Su biyun nan duka 'yan uwana ne, uwarmu daya ubanmu daya....

BARKA DA SABUWAR SHEKARAR 2017



Abdullahi ya dukar da kansa kasa a gaban Halifa ya ce, "Ya Halifan Allah, wadannan ba karnuka ba ne face samari biyu, ma'abuta kyawu da cikar halitta da kwarjini da daidaito. Su biyun nan duka 'yan uwana ne, uwarmu daya ubanmu daya." Halifa ya tambaye shi cikin mamaki, "Yaya dan Adam zai koma siffar kare?" Abdullahi ya amsa, "Ka yi mini izini, ya Shugaban Muminai, in labarta maka da gaskiyar labarinsu" Halifa ya ce, "Fada mini labarinsu, amma na hore ka da ka gaya mini gaskiya domin ita ce jirgin tsirar kowane mutum, ita ce alamar managarta daga cikin mutane." Abdullahi ya ce, "Ya Halifan Allah bisa ga bayan kasa, zan fada maka gaskiya a gaban wadannan karnuka, idan na yi gaskiya za su shaide ni, idan kuma na yi karya za su karyata ni a gabanka." Halifa ya dube shi, "Wadannan ai karnuka ne, ta yaya za su yi magana balle su gasgata ka, ko su karyata ka?" Abdullahi ya dubi karnuka ya ce, "Ya 'yan uwana, idan na fadi karya ku rauda kawunanku kuna kyibta idanu. Idan kuma na fadi gaskiya ku sunkuyarda kawunanku kasa kuna lumshe idanu." Daga nan sai Abdullahi dan Falilu ya fara labari ya ce, ya Halifa, ka sani mu uku muke 'yan uwan juna, uwarmu daya, ubanmu daya. Sunan mahaifinmu Falilu. An rada masa wannan suna ne saboda su biyu uwarsu ta haife su tare, 'yan tagwaye. Daya ya mutu nan take, mahaifinmu ya wanzu. Don haka sai mahaifinsa ya sanya masa suna Falilu, watau wanzajje. Mahaifinsa ya rene shi har zuwa girmansa, ya yi masa aure da mahaifiyarmu, sa'annan ya kwanta ya mutu. Yayin da mahaifiyarmu ta sami ciki sai ta haifi wannan dan uwan nawa na farko, aka sanya masa suna Mansur. Ta sake samun ciki, ta haifi wannan dan uwan nawa na biyu, mahaifinmu ya rada masa suna Nasiru. Da ta sake samun ciki na uku sai aka haife ni, mahaifina ya sanya mini suna Abdullahi. Mahaifinmu ya rene mu tare cikin tsananin kulawa har sai da muka isa munzalin mutane, sai ya kwanta ciwon ajali ya mutu. Ya bar mana gadon gida da rumfarsa ta kasuwa wacce take cike da dukiya ta daga dukkan tufafin Hindu,da na Rum, da na Hurassana, da wadansun wadannan, tare da tsabar kudi har dinari dubu sittin. Muka wanke gawar mahaifinmu, muka yi masa jana'iza, muka kai shi masaukinsa na karshe, muka gina kubba mai girma a wurin domin girmamawa gare shi. Muka gayyaci malamai wurin kabarinsa, suka yi ta sauke Kur'ani mai girma tsawon kwanaki arba'in domin nema masa gafara, da nema masa tsari daga shiga wuta. Bayan an yi sadakar arba'in sai na gayyaci dukkan tajirai da manyan gari na shirya musu walima, aka ci aka sha aka tumbatsa. Da aka gama cin abinci sai na mike na ce musu, "Ya ku mutane, ku sani cewa wannan duniya ba matabbata ba ce, lahira ita ce gidan dawwama. Girma da daukaka sun tabbata ga wannan wanda ba ya gushewa har abada. Shin ko kun san dalilin da sa ya sa na kira ku nan, a cikin wannan rana mai albarka?" Suka amsa mini, "Allah shi ne masani a dukkan abin da yake boye." Na ce musu, "Mahaifina ya mutu ya bar kudi masu yawa, to ban sani ba ko akwai wanda ke bin sa bashi daga cikinku. Idan akwai mai bin sa bashi sai ya yi magana ya ce, 'ina bin sa abu kaza da kaza' ni kuwa in biya shi saboda in sauke masa nauyin da ke kansa wanda bai sami saukewa ba." Dukkansu suka amsa mini, "Ya Abdullahi, hakika duniya gidan rudi ce, lahira ita ce gidan tabbata. Wane kinibibi zai sa mu ce muna bin mahaifinka bashi, don dai son abin duniya. Dukkanmu mun san cewa cin dukiyar marayu babban laifi ne. Allah ya ji kan mahaifinka da rahama, ba mu san mai bin sa bashi ba, shi ne ma ke biyar mutane da yawa. Mahaifinka ba abin da ya ke gudu irin cin bashi, sau da yawa mukan ji shi yana addu'a, 'Allah ka tsare da cin bashi, Allah ka da ka dauki raina da bashin mutane ga wuyana.' Dukkanmu shaidu ne, idan ya dauki bashin mutum, nan da nan yake biyansa ba tare da mai kayan ya matsa masa ba. Idan kuwa kayansa aka dauka bashi, to ba ya takura wa wanda ya amshi kayan, idan ma talaka ne sosai sai ya yafe masa. Idan kuma ba talaka ba ne kuma mutumin ya mutu bai biya shi ba sai ya ce, 'na yafe masa,

Wednesday

HIKAYAR BIRNIN DUWATSU 02.

Abullahi dan Falilu ya kwanta kusa gare shi, amma a nasa gadon daban. Abu Is'haka ya kwanta kamar zai yi barci amma barcin bai dauke shi ba. Sai ya yi ta karatu a cikin zuciyarsa, wani lokaci kuma sai ya rera baitoci a kan sha'anin rayuwa. Da ma shi mutum ne gwanin hikima, ga shi kuma gwanin bayar da labari, shi ya sa Halifa ke son sa kwarai da gaske har ya sanya shi daya daga cikin amintattunsa. Haka ya ci gaba da karatunsa yana rera wakoki har zuwa talatainin dare....

CIGABA


Daga nan sai ya ga Abdullahi dan Falilu ya tashi daga kan gadonsa, ya daura damara ga kugunsa, ya bude wani dan akwati ya dauki bulala da shama'a kunnaniya, ya fice daga cikin soron da suke kwance, yana tsammani bakonsa barci yake yi. Yayin da Abu Is'haka ya ga haka sai mamaki ya kama shi, ya ce a cikin ransa, "Ina Abdullahi dan Falilu za ya da bulala cikin dare? Yalla ko yana nufin ya azabta wani. Bari dai na bi shi in ga abin da zai yi cikin wannan tsohon dare." Yayin nan Abu Is'haka ya tashi ya bi bayansa yana sanda a hankali yadda ba za a ji tafiyarsa ba. Ya ga Abdullah ya bude taska ya fito da kabaki daga cikinta da tasoshi hudu a gabansa cike da waina da nama, da kasaken ruwa. Ya dauki kabakin ya tafi, Abu Is'haka ya ci gaba da bin sa a hankali, har ya shiga daki. Da Abu Is'haka ya ga ya shiga cikin daki sai ya ja ya tsaya daga bakin kofa, ya zama yana leken cikin dakin. Ya ga dakin mayalwaci, an shimfide shi da shimfidu na alfarma. A tsakiyar dakin an kafa gado na li'aji zananne da zinariya,a jikin gadon an daure karnuka biyu da sarkoki na zinariya. Abdullahi ya ajiye kabaki daga kuryar daki, ya zare damuttsansa, ya kwance kare na farko. Kare ya zama yana wutsilniya yana turmusa hancinsa ga kasa, ka ce shi yana sumbatar kasa ne gaba ga Abdullahi, yana kuka kasa-kasa da murya mai mai ban tausayi. Duk wannan abu da karen nan ke yi, Abdullahi bai kula ba, ya ride shi ya buga ga kasa, ya daure kafafun. Ya zari bulala ya sabkar masa da bugu, bugu mai karfi ba da tausayi ba. Kare ya yi ta wutsilniya yana kuka, kuka mai tsanani, amma Abdullahi bai dakata da bugun sa ba har sai da ya ji ya bar motsi ya suma. Yayin nan ya ja shi kasa ya kai ga gadon nan ya daure shi ga bigirensa. Ya kwance kare na biyu, ya aikata bugu gare shi kamar yadda ya yi wa na fari. Daga nan sai ya ciro adiko ya riga goge musu jikinsu yana ba su hakuri yana cewa, "Kada ku rike ni da wannan abu, ba da son raina na aikata muku shi ba. Allah ya ba ku sauki ya kawo muku mafita." Ya ci gaba da yi wa karnukan nan addu'ayana shafa jikinsu. Duk wannan abu da ke faruwa, Abu Is'haka amintaccen Halifa na make bakin kofa yana leke da idanunsa yana kuma ji da kunnuwansa, yayi mamakin wannan abu matukar mamaki.


KU BIYO MU DON CIGABAN WANNAN LABARI

Tuesday

HIKAYAR BIRNIN DUWATSU 01

Wata rana Halifa Haruna Rashid na duba harajin da sarakuna da hakimansa suka aiko da shi cikin wannan shekara, sai ya lura cewa Sarkin Basara ne kadai bai aiko da nasa harajin ba. Don haka sai Halifa ya tara 'yan majalisarsa. Da suka taru sai ya ce, "Ina Waziri Ja'afaru?" Waziri Ja'afaru ya zo kusa ga Halifa ya tsaya ya ce, "Ga ni, Allah ya daukaki mulkinka." Halifa ya ce, "Harajin kowane sarki da ke karkashina ya shiga baitulmali, amma babu harajin Basara." Ja'afaru ya dukar da kai ya ce, "Ya Shugaban Muminai, watakila akwai wani babban al'amari da ya faru ga Sarkin Basara da ya sa shi sha'afa da aiko da nasa harajin." Halifa ya ce, "Yau kwana ashirin da gama tattara haraji, idan har wani al'amari ya same shi, mi ya sa bai aiko mana ba, domin mu san halin da yake ciki?" Waziri ya amsa masa, "Allah ya taimake ka, ina ganin mu aika masa da manzo wanda zai dawo mana da labari." Halifa ya ce, "Ka tura Abu Is'haka al- Mausili, daya daga cikin amintattunmu." "Na ji, na amince.Ina mai biyayya ga Allah, ina mai biyayya gare ka, ya Shugaban Muminai." In ji Ja'afaru. Nan da nan sai Ja'afaru ya sa aka kira masa Abu Is'haka zuwa gidansa. Da ya zo sai ya rubuta takarda a madadin Halifa, ya ba shi ya ce, "Karbi wannan takarda ka kai wa Abdullahi dan Falilu, Sarkin Basara. Halifa ya duba dukkan harajin da sarakunansa suka aiko amma bai ga na Sarkin Basara ba. Idan ya tattara harajin ka karbo ka dawo mini da shi, idan kuwa bai tattara ba, to ka zo tare da shi, ya fada wa Halifa da bakinsa abin da ya hana shi aiko da nasa haraji." Abu Is'haka ya ce, "Na ji, na amince." Waziri Ja'afaru ya hada shi da mahaya dubu biyar suka nufi Basara. Yayin da suka yi kusa da birnin Basara sai Abdullahi dan Falilu ya sami labarin zuwansa. Nan take ya fita da runduna ya tarye shi, suka dawo cikin birni tare, har suka isa fada. 'Yan rakiya kuma sai suka kafa tantuna a bayan gari, aka aika musu da dukkan abin da suke bukata na abinci da abin sha da shimfidu.Lokacin da Abdullahi dan Falilu da Abu Is'haka suka shiga fada, sai Abu Is'haka ya zauna bisa karaga, ya zaunar da Abdullahi dan Falilu kusa gare shi. Wazirai da fadawa kowa ya zauna gwargwadon matsayinsa. Da fada ta nutsu, sai Abdullahi dan Falilu ya mike. Bayan ya yi sallama da gaisuwa ga Abu Is'haka sai ya ce, "Ya shugabana, ko akwai wani sako ne da ka zo mana da shi?" Bako ya amsa, "I. Na zo ne domin na karbi harajin kasarka. Kowa ya aika da harajinsa amma Halifa bai ga naka ba, ga shi har lokacin karba ya wuce." Abdullah dan Falilu ya yi murmushi ya ce, "Allah Sarki, an ce rashin sani ya fi dare duhu. Da ka sani da ba ka walar da kanka garin zuwa ba. Haraji na nan na kammala hadawa, da gobe nake niyyar aikawa da shi. Amma tun da ka zo zan damka shi ga hannunka, ka wuce wa Halifa da shi. Yanzu sai ka zauna ka huta zuwa kwana uku, mu shirya maka liyafa ta musamman domin karramawa da kuma girmama Halifa, a kwana na hudu sai na ba ka harajin tare da tsarabar da za ka tafi da ita." Abu Is'haka ya ce, "Babu laifi ga wannan." Daga nan sai Abdullahi dan Falilu ya sallami kowa. Da aka watse sai ya ja bakonsa zuwa wani kayataccen soro da babu kamarsa ga kyawu. Ya sa aka jera akussan abinci domin Abu Is'haka da manyan na hannun damarsa. Suka ci suna raha har suka bankare cikannansu. Da suka koshi sai aka kawar da akussa aka jera gorunan gahawa da abin sha. Suka yi ta sha suna hira, ba su ankara ba har dare ya raba. Aka shirya wa Abu Is'haka shimfida mai taushi bisa gadon zumarrazi da aka shafe da ruwan zinariya mai kyalkyali. Abullahi dan Falilu ya kwanta kusa gare shi, amma a nasa gadon daban. Abu Is'haka ya kwanta kamar zai yi barci amma barcin bai dauke shi ba. Sai ya yi ta karatu a cikin zuciyarsa, wani lokaci kuma sai ya rera baitoci a kan sha'anin rayuwa. Da ma shi mutum ne gwanin hikima, ga shi kuma gwanin bayar da labari, shi ya sa Halifa ke son sa kwarai da gaske har ya sanya shi daya daga cikin amintattunsa. Haka ya ci gaba da karatunsa yana rera wakoki har zuwa talatainin dare....

KU KASANCE TARE DAMU DON CIGABA.
GASKIYA DA GASKIYA BA MAGANAR YAUDARA DA FATAN ZAKU FAHIMCE NI.

Thursday

1. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO

An yi wani mutum a cikin Birnin Bagadada, lokacin mulkin Halifa Haruna Rashid, mai suna Sindibad. Wannan mutum ya kasance talaka ne, ba shi da wata sana’a sai dako – watau ya rika daukar wa mutane kaya bisa kansa daga wani wuri zuwa wani wuri ana biyansa. Wata rana Sindibad ya yi dakon wasu kaya masu nauyi, lokacin kuwa ana koda rana, kafin ya isa wurin da zai kai kayan nan ya yi gumi sharkaf, ga shi kuma ya gaji likis, sai ya biyo ta gaban wani babban gida. Da ganin wannan gida na wani babban attajiri ne, mai ji kudi. An share gaban gidan tas, an zuba wa shuke-shuken da ke wurin ruwa. Kodayake ana tsananin zafin rana amma gaban wannan gida sai wata iska mai sanyi ke kadawa kamar lokacin hunturu. Sindibad ya hangi wani dandamali a gaban gidan cikin shuke-shuken nan, ya ce a ransa, “Bari in dan zauna wurin nan in sarara kadan.” Ya ajiye kayan dakonsa ya zauna bisa dandamali yana kwasar sassanyar iskar da ke tashi, sai ya ji wani irin kamshin abinci mai dadi na jifarsa daga cikin gidan nan. Can kuma sai ya rika jin kidan molo da busar sarewa na tashi. Ya jiyo muryoyin ‘yan mata na rera wakoki, sai dai bai jin abin da suke fada saboda nisa. Daga cikin lambun gidan kuma tsuntsaye ne iri-iri bisa furannin suna ta rera nasu wakoki. Da ya duba kasa kuma sai ya ga wadansu ‘yan kananan kwari masu ban sha’awa suna ta kai da komowa a cikin ciyawar da ta fito kasan furannin. Sindibad ya yi mamaki matuka da yadda Allah mai girma da daukaka ya tsara wadannan abubuwa daki-daki, kowane gwanin ban sha’awa. Zuciyarsa ta yi fari bisa ga wadannan abubuwa da ke debe masa kewa. Amma kuma da ya tuna da halin da yake ciki na talauci sai ransa ya baci. Ya tashi ya leka cikin lambu sai ya hango bayi suna ta aiki sai ka ce gidan wani Sarki, wasu na ban ruwa, wasu na nome ciyayi, wasu na tsinkar ‘ya’yan itace. Hancinsa kuwa ya ce me zai shaka in ba kamshin soyayyen nama ba.
Sindibad Dandako
Da Sindibad ya ga irin wannan daula da mai gidan nan ya ke ciki sai ya daga hannayensa sama yana cewa, “Godiya ta tabbata gare ka ya Ubangijin talikai, mai arzuta wanda ya so a lokacin da ya so. Ya Ubangiji ina rokonka, ka yafe mini dukkanin zunubaina, gare ka kadai nake neman gafara. Ya Ubangiji kai ne mai yin yadda ka so ba tare da shawarar kowa ba, kuma babu wanda ya isa ya tambaye ka don me. Kai ne Ubangijin sammai da kassai da abin da ke tsakaninsu. Kai ne mai arzuta wanda ka so, ka kuma talauta wanda ka so. Kai ne mai daukaka wanda ka so, ka kuma kaskanta wanda ka so. Na tabbata babu wani abin bauta wa da gaskiya sai kai. Hakika kana daukaka wanda ka so kamar yadda ka daukaka ma’abucin wannan gida. Kana talauta wanda ka so kamar yadda na tsinci kaina a ciki.” Sai ya wake wadannan baitoci:
Mutum nawa ke wahala tamkata,
Ga wasu sai hutu da sakewa.
Kowace rana ga ni wahalce,
Dauke da kaya babu dagawa.
Dubi wadansu suna nan kwance,
Kullum shan gara da dadawa.
Ba su tunanin daukar kaya,
Mai nauyi ko mai sabawa.
Asalinmu da kai duka daya ne,
Ruwa na maniyi mai turawa.
Banbancinmu akwai shi da dama,
Tamkar na madaci ko zumuwa.
Ya Allahu gare ka na roka,
Ba ka zalunci cutarwa.
Lokacin da Sindibad dan dako ya gama rera wannan waka sai ya dauki kayan dakonsa ya dora a kai zai tafi. Sai ga wani bawa ya fito daga cikin gidan, mai kyakkyawar fuska da madaidaicin jiki, da tufafi na alfarma. Ya kama hannun dan dako ya ce, “Shigo ciki shugabana na kira.”
Dan dako ya yi tsaye ya ki shiga cikin gida, ya ce wa bawa shi sauri yake yi ya kai kayan da ke bisa kansa. Bawa ya ce babu makawa sai ya shiga cikin gida. Da dai ya ga bawan nan ba zai bar shi ya tafi ba sai ya ajiye kayansa a bakin kofa, inda wani bawa ke gadi, ya bi bawan da aka aiko suka shiga cikin gida tare. Dan dako ya yi ta ware ido yana kallon kayan kawar da aka sanya a cikin gidan. Suka shiga cikin wani babban dakin shakatawa, suka tarar da mutane zazzaune bisa ababen zama, kowane daga cikinsu yana sanye da tufafi na alfarma masu tsadar gaske. Kallo daya za a yi musu a gane cewa babu daya daga cikinsu da ya san wani abu wai shi talauci. A gaban kowane mutum an ajiye akushin nama, da goran abin sha, da ‘ya’yan itace, da furanni masu kamshin gaske. Ga kuma kuyangi kyawawa suna kada molo suna waka da rawa a gaban wadannan mutane. Mutanen nan na zaune ne sahu-sahu, gwargwadon yawan dukiyar kowa. Manyan attajirai su ne a sahun farko, masu bi musu a sahu na bayansu, su ma masu bi musu a sahun bayansu. A gaban sahun farko akwai wani mutum dattijo mai tsawon gemu, wanda hurhura ta fara fitowa jefi-jefi a cikin gemun. Tufafinsa sun fi duka na sauran mutanen da ke wurin kyau. Yana da fuska mai annuri da yawan fara’a. Ga shi da kwarjini da farin jini. Wannan mutum dai shi ne mai wannan gida. Sindibad dan dako ya dubi dakin shakatawar nan ya yi ajiyar zuciya, ya ce a cikin ransa, “Wallahi da a ce mutuwa na yi, na tashi na gan ni a wannan wuri, da na ce Aljanna ce. Babu shakka wannan wuri fadar wani babban Sarki ce, inda yakan zo domin shakatawa.” Ya matsa gaban dattijon nan da ke gaban mutane ya durkusa ya gaishe shi, ya kuma gayar da sauran attajiran da ke cikin dakin. Ya mike tsaye a gabansu kansa a sunkuye yana duban kasa. Shugaban attajiran, dattijon da yake zaune a gaban sauran attajirai, ya umurci dan dako ya matso kusa gare shi. Ya yi masa barka da zuwa sa’annan ya sa aka kawo masa abin zama, ya umurce shi da ya zauna. Bayan ya zauna sai aka kawo masa abinci da abin sha. Dan dako ya wanke hannunsa, ya yi bismillah ya gini abinci har sai da ya kai masaba gatari. Ya wanke hannunsa ya yi hamdala, ya kuma yi wa attajirai godiya.
Mai gida ya ce masa, “Mun yi murna da zuwanka. Amma menene sunanka?”
Dan dako ya ce, “Ya shugabana, sunana Sindibad dan dako. Amma Sindibad din har ya kusa bacewa sai dai a kira ni da dan dako, domin ita ce sana’ata.”
Mai gida ya wangame baki, alamun mamaki, ya ce, “Ka kuwa ga sunanmu daya da kai. Ni ma sunana Sindibad bahariyi ko kuma mai teku. Ana kirana da mai teku ne saboda yawan tafiye-tafiyen da na yi a cikin teku. Ko za ka rera mana wakar nan da muka jiyo kana rerawa a waje?”
Dan dako ya sunkuyar da kansa cikin jin kunya, ya ce, “Ya shugabana, ka sani cewa idan talauci ya dabaibaye mutum bai san lokacin da yake furta wasu kalamai ba.”
Mai gida ya ce, “Kada ka ji kunya, ai yanzu ka zama dan uwana. Na ji dadin wakar ne lokacin da kake rera ta, shi ya sa nake so ka kara rera mini ita yanzu.” Dan dako ya karkace kai ya kara rera waka. Yayin da sauran tajirai suka ji wannan waka sai suka cika da mamaki.
Mai gida ya ce, “Ka sani ya kai dan dako, labarina abin mamaki ne. Zan gaya maka irin wahalhalun rayuwar da na shiga har Allah ya ba ni wannan tarin dukiya da kake gani. Kamar yadda ka ji ana cewa, zomo ba ya kamuwa daga zaune, to, wannan gaskiya ne. Domin na sha wahalar rayuwa iri daban-daban, kafin in zama yadda nake yanzu. Ba don Allah ya kaddara ina da tsawon kwana ba ai da tuni an manta da ni saboda hadurran da na shiga Allah ya kubutar da ni. Na yi tafiye-tafiye har guda bakwai a cikin teku, kowace tafiya daya tana kunshe da labari mai ban tu’ajjibi. Kamar yadda na ce ma ba don Allah ya kaddare ni da tsawon kwana ba da tuni na halaka a cikin wadannan tafiye-tafiye.” Daga nan sai Maigida ya daga murya da karfi, yadda duk wanda ke cikin dakin ke iya jin sa, ya ce, “Ya ku abokaina attajirai, yau zan gaya muku labarin tafiye-tafiyen da na yi guda bakwai masu hatsarin gaske da ban mamaki a cikin teku.” Sai ya ci gaba da labari:
TAFIYAR SINDIBAD TA FARKO A CIKIN TEKU
Mahaifina attajiri ne na gaske mai ji da sulalla. Dukkan mutanen gari na son shi saboda yawan kyautarsa da kyawun dabi’unsa. Babban abin da ke ba mutane mamaki game da mahaifina shi ne duk da tarin dukiyar nan tasa ba ya da girman kai ko kadan. Ban girma na yi wayo tare da mahaifina ba, ya rasu lokacin da nake yaro, ya bar mini gadon tarin kudinsa da gidaje da gonaki, kasancewar ni kadai ne dan da ya haifa.
Da na girma na yi wayo, sai idona ya bude da kudi. Na shiga cikin dukiyar nan ina bundum-bundum. Ba na cin abinci sai lafiyayye mai kyau mai tsada, haka ma abin sha. Sutura kuwa sai irin ta ‘ya’yan Sarakuna nake sanyawa. Wurin da nake kwanciya kuwa ko sarauniyar duniya duka sai haka. Na yi abokai da yawa, kullum sai in ta kashe musu gara suna kwasa a fayu. Su kuwa sai su yi ta zuga ni suna tara mini kasa ina hayewa, ina jin dadi. Ni kuwa na ci gaba da facaka da dukiya, a tsammanina ba za ta taba karewa ba. Haka na dawwama tsawon wani lokaci, har aka wayi gari ran nan ko dirhami bai rage mini ba. To, wanda ma ya tattali dukiya ya ya kare da ita, balle ni da na shiga barnatar da ita?
Ko da na farga lokaci ya kure mini, domin ban da gidan da nake ciki babu wani abu da ya rage mini na dukiya. Hankalina fa ya tashi, ga abokaina duk sun guje mini saboda yanzu ba ni da sule. Da ma an ce kuda ba ku biyar mai kayan gawai. Ban ga laifinsu ba, domin hannu mai miya ake lasa. Wata rana na yi zaune zugum ina tunanin inda zan sami dan dirhamin da zan sayi abinci, sai maganar Shugaba Sulaimanu Dan Dawuda (Tsira da amincin Allah ya tabbata a gare su) wadda nakan ji mahaifina yana yawan karantawa ta fado mini, “Gwamma abu uku da abu uku: gwamma ranar mutuwa da ranar haihuwa; gwamma kare mai rai da mataccen zaki; gwamma shiga kabari da bakin talauci.”
Da na tuna da wannan magana sai na tashi na tattara ‘yan sauran komatsan da na mallaka har da suturata duka, na kai kasuwa na sayar a kan kudi dirhami dubu uku. Niyata in bi fatake in shiga duniya wurin fatauci, domin an ce babu maraya sai raggo, kuma sai an nema akan samu.

Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar littafin DARE DUBU DA DAYA. Daga yanzu zuwa kowane lokaci littafin zai shiga kasuwa.

Za mu ci gaba a kashi na 2.