Wane kinibibi zai sa mu ce muna bin mahaifinka bashi, don dai son abin duniya. Dukkanmu mun san cewa cin dukiyar marayu babban laifi ne. Allah ya ji kan mahaifinka da rahama, ba mu san mai bin sa bashi ba, shi ne ma ke biyar mutane da yawa. Mahaifinka ba abin da ya ke gudu irin cin bashi, sau da yawa mukan ji shi yana addu'a, 'Allah ka tsare da cin bashi, Allah ka da ka dauki raina da bashin mutane ga wuyana.' Dukkanmu shaidu ne, idan ya dauki bashin mutum, nan da nan yake biyansa ba tare da mai kayan ya matsa masa ba. Idan kuwa kayansa aka dauka bashi, to ba ya takura wa wanda ya amshi kayan, idan ma talaka ne sosai sai ya yafe masa. Idan kuma ba talaka ba ne kuma mutumin ya mutu bai biya shi ba sai ya ce, 'na yafe masa,
CIGABA.......
Allah ya yafe masa laifukansa.' Don haka muna da tabbacin babu mai bin sa komai." Yayin da na ji haka sai na ce musu, "Na gode, Allah ya yi muku albarka." Daga nan sai na juya wurin wadannan 'yan uwa nawa na ce musu, "To kun ji, babu mai bin mahaifinmu bashi. Kun dai sani ya bar mana kudi masu yawa da gida da rumfa cike da kaya. Tun da mu uku ne, ke nan za a kasa dukiyar kashi uku kowa ya dauki kashi guda. Me kuka gani yanzu? Mu bar dukiyar yadda take muna juya ta tare, mu ci mu sha tare, ko kuwa a raba kowa ya dauki rabonsa ya shiga juyawa da kansa?" Suka ce mini, "Mun fi so a raba kowa ya dauki kasonsa." Abdullahi dan Falilu ya dubi karnuka ya ce, "Haka aka yi, ya 'yan uwana?" Suka sunkuyar da kai kasa suka lumshe ido, suna ishara da cewa, "Haka ne." Abdullahi ya ci gaba da labari ya ce, sai na kira wakilin alkali, ya Shugaban Muminai, ya raba mana dukkan dukiyar da mahaifinmu ya bari da kudi. Gida da rumfa suka fada cikin rabona, saboda 'yan uwana sun ce sun fi son tsabar kudi.Dukkanmu muka amince da wannan rabo, 'yan uwana suka kwashi kudi cunkus, ni kuwa aka bar mini gida da rumfa da 'yan kudi kadan, wadanda na sayi kayayyaki na zuba cikin rumfar, na zauna ina saye ina sayarwa. Amma 'yan uwana sai suka sayi haja mai yawa, suka dauki ijarar jirgin ruwa suka nufi wurin fatauci cikin duniya nesa da garinmu. Na yi musu addu'a, 'Allah ka yi musu budi, ni kam na fi so in zauna gida lafiya. Tsiya da kwanciyar hankali ya fi arziki da tashin hankali.' Na zauna tsawon shekara guda cikin rumfata, tswaon wannan lokaci kuwa Allah ya bude mini kofofin arziki, na sami riba ninkin-ba-ninkin, na tara dukiya kamar yadda mahaifinmu ya bar mana. Wata rana da hunturu, ana zazzaga sanyi, ina zaune cikin rumfata, na sanya riguna biyu, na gashi mai taushi, masu tamanin gaske, sai ga 'yan uwana sun zo gare ni. Kowane daga cikinsu na sanye da tsummar riga, duk ta kekkece har ana ganin fatar jikinsu. Ga lebbansu sun yi fari fat sun bushe, jikinsu sai makyarkyata yake yi saboda sanyin da ke bugun su...
www.shulaman.wapka.me
Wata rana da hunturu, ana zazzaga sanyi, ina zaune cikin rumfata, na sanya riguna biyu, na gashi mai taushi, masu tamanin gaske, sai ga 'yan uwana sun zo gare ni. Kowane daga cikinsu na sanye da tsummar riga, duk ta kekkece har ana ganin fatar jikinsu. Ga lebbansu sun yi fari fat sun bushe, jikinsu sai makyarkyata yake yi saboda sanyin da ke bugun su. Yayin da na gan su cikin wannan hali sai hankalina ya tashi, nan take tausayinsu ya kama ni. Na mike da sauri na rungume su ina hawaye. Na cire rigunan da na sanya na gashi na sanya wa kowannensu. Na ja su zuwa gidan wanka, na aika musu da tufafi masu tsada irin na tajirai, kowace tufa, tamaninta dinari dubu. Bayan sun yi wanka sun sanya tufafin da na ba su, sai na tafi da su zuwa gidana, na dauko kabakin abinci na girke musu, domin na lura da suna cikin matsananciyar yunwa. Na zauna muka ci abinci tare ina debe musu kewa da labarai na nishadi. Abdullahi ya juya ga karnuka ya tambaye su, "Haka aka yi, ya 'yan uwana?"Suka sunkuyar da kawunansu kasa suna lumshe idanu, suna cewa da ishara, "Haka ne!" Abdullahi ya ci gaba, yayin da suka ci suka koshi, ya Halifan Allah, sai na tambaye su, "Me ya faru gare ku? Ina dukiyarku?" Suka amsa mini, "Bayan mun yi cikon haja sai muka dauki jirgi muka fada cikin kogin Dujillati muka yi ta tafiya har muka iso ga wani gari mai suna Kufa, inda muka rika sayar da hajarmu da riba mai yawa, duk abin muka saye rabin dinari sai mu sayar da shi dinari goma, abin dinari guda kuwa muka sayar da shi dinari ashirin. Muka sami riba mai yawa wadda ba mu san iyakarta ba. Da muka sayar da hajar mu duka sai muka sayi haja irin ta Farisa. Abin da ake sayar wa a nan Basara dinari arba'in, a can sai muka saye shi dinari goma, da niyyar idan muka dawo nan mu ci riba daga gare shi. Daga Kufa muka shiga jirgi sai wani gari da ake kira Karhi, a nan ma muka saye muka sayar, muka sami riba mai dimbin yawa." Haka suka ci gaba da gaya mini garuruwan da suka tafi da irin ribar da suka samu. Saina tambaye su, "To, tun da kun sami irin wannan sa'ar fatauci, ya aka yi na gan ku cikin halin da kuka dawo?" Suka yi ajiyar zuciya, suka ce, "Ya dan uwanmu, muna tsammani wani mai kandun baka ne ya yi mana baki, ka san mutane ba su iya ganin abu su yi kurum. Bayan mun sami dukiya mai yawa daga wannan fatauci sai muka yi nufin dawowa gida. Muka sami babban jirgi muka sanya kayanmu, muka yi wa Basara tsinke. Muka kwana uku muna tafiya, a rana ta hudu sai bahar ta canja mana fuska. Ta tashi da hauka, tana toroko tana raurawa, iska mai karfi na kada ruwa, tozaye na tashi suna marin juna da wata irin kara kamar aradu da tartsatsi kamar na wuta a cikin duhun dare. Iska ta karkatar da jirginmu daga barin tafarki, ta kwashe shi ta fyada ga wani dutse da ya taso saman ruwa. Jirgi ya tarwatse dukkan dukiyarmu ta dulmiye cikin ruwa, muka yi ta kokarin ceton rayukanmu tsawon kwana daya da yini guda. Daga nan sai Allah ya koro mana da wani jirgi, matukansa suka taimake mu. Da muka sami kanmu sai mukanufo Basara, muna tafe muna bara daga wannan gari zuwa wancan. Muka sayar da tufafin jikinmu muka ci abinci, mun sha bakar wahala, wadda ba ta misaltuwa, a kan hanya kafin mu iso nan. Da a ce Allah ya nufa mun dawo da dukiyar da muka samu gida, to da ba za a sami mai kamarta ba duk garin nan, sai fa Sarki. Sai dai abin da Allah ya hukunta zai sami bawansa, to babu mai ikon ije shi." Na ce musu, "Ya 'yan uwana, kada wannan abu ya dame ku, ku gode wa Allah da ya tsirar da rayukanku. Idan da rai ai bawa ba ya yanke kauna. Wa ya sani ko a nan gaba ku sami wata dukiyar fiye da wadda kuka samu a baya." Na ci gaba da cewa, "Ya 'yan uwana, ku kaddara cewa kamar yau ne mahaifinmu ya mutu, wannan dukiya da ke hannuna tasa ce. Ina so mu sake raba ta daidai kamar yadda aka yi a baya." Na kira wakilin alkali na ce masa ya raba mana dukiyar nan a tsakaninmu. Ya kuwa raba mana ita kashi uku daidai, kowa ya dauki kashi guda. Na ce musu, "Ya 'yan uwana, Allah shi ne mai arzutta bawa a kowane gari yake.Kowane dayanku ya bude rumfa a cikin kasuwa ya zauna cikinta, watakila wannan ya zama silar arzikinku domin Allah shi ne masanin gaibi." Na taimaka musu suka bude rumfuna, suka saisayi kayayyaki suka zuba a ciki. Na ce musu, "Ku saya ku sayar, ku rika boye ribar kada ku barnatar, dukkan abin da kuke bukata na abinci da nama da abin sha, to ku yi mini magana zan ba ku." Na ci gaba da tarairayar su ina kara musu kwarin gwiwa a kasuwancinsu. Suka zama kullum suna bude rumfunansa da safe har zuwa yamma, yayin nan sai su rufe su dawo gidana mu ci abinci da abin sha tare, sa'annan mu kwanta. Ban taba bari suka taba kudinsu ba, komai suke so ni ke yi musu cikin kudina. Amma duk lokacin da muka zauna hira, babu zancen da suke yi sai na su dai suna son zuwa fatauci, zama wuri daya ya ishe su. Sai su yi ta ba ni labarin irin dukiyar da ake samu a fatauci, suka yi ta lallashina wai mu tafi tare in gani da idona. Suka ce wai muddin na dandana dadin da ke ga fatauci ba zan kara yarda na zauna gida ba kamar mace.
No comments:
Write Comments