Wednesday

Home HIKAYAR BIRNIN DUWATSU 02.
Abullahi dan Falilu ya kwanta kusa gare shi, amma a nasa gadon daban. Abu Is'haka ya kwanta kamar zai yi barci amma barcin bai dauke shi ba. Sai ya yi ta karatu a cikin zuciyarsa, wani lokaci kuma sai ya rera baitoci a kan sha'anin rayuwa. Da ma shi mutum ne gwanin hikima, ga shi kuma gwanin bayar da labari, shi ya sa Halifa ke son sa kwarai da gaske har ya sanya shi daya daga cikin amintattunsa. Haka ya ci gaba da karatunsa yana rera wakoki har zuwa talatainin dare....

CIGABA


Daga nan sai ya ga Abdullahi dan Falilu ya tashi daga kan gadonsa, ya daura damara ga kugunsa, ya bude wani dan akwati ya dauki bulala da shama'a kunnaniya, ya fice daga cikin soron da suke kwance, yana tsammani bakonsa barci yake yi. Yayin da Abu Is'haka ya ga haka sai mamaki ya kama shi, ya ce a cikin ransa, "Ina Abdullahi dan Falilu za ya da bulala cikin dare? Yalla ko yana nufin ya azabta wani. Bari dai na bi shi in ga abin da zai yi cikin wannan tsohon dare." Yayin nan Abu Is'haka ya tashi ya bi bayansa yana sanda a hankali yadda ba za a ji tafiyarsa ba. Ya ga Abdullah ya bude taska ya fito da kabaki daga cikinta da tasoshi hudu a gabansa cike da waina da nama, da kasaken ruwa. Ya dauki kabakin ya tafi, Abu Is'haka ya ci gaba da bin sa a hankali, har ya shiga daki. Da Abu Is'haka ya ga ya shiga cikin daki sai ya ja ya tsaya daga bakin kofa, ya zama yana leken cikin dakin. Ya ga dakin mayalwaci, an shimfide shi da shimfidu na alfarma. A tsakiyar dakin an kafa gado na li'aji zananne da zinariya,a jikin gadon an daure karnuka biyu da sarkoki na zinariya. Abdullahi ya ajiye kabaki daga kuryar daki, ya zare damuttsansa, ya kwance kare na farko. Kare ya zama yana wutsilniya yana turmusa hancinsa ga kasa, ka ce shi yana sumbatar kasa ne gaba ga Abdullahi, yana kuka kasa-kasa da murya mai mai ban tausayi. Duk wannan abu da karen nan ke yi, Abdullahi bai kula ba, ya ride shi ya buga ga kasa, ya daure kafafun. Ya zari bulala ya sabkar masa da bugu, bugu mai karfi ba da tausayi ba. Kare ya yi ta wutsilniya yana kuka, kuka mai tsanani, amma Abdullahi bai dakata da bugun sa ba har sai da ya ji ya bar motsi ya suma. Yayin nan ya ja shi kasa ya kai ga gadon nan ya daure shi ga bigirensa. Ya kwance kare na biyu, ya aikata bugu gare shi kamar yadda ya yi wa na fari. Daga nan sai ya ciro adiko ya riga goge musu jikinsu yana ba su hakuri yana cewa, "Kada ku rike ni da wannan abu, ba da son raina na aikata muku shi ba. Allah ya ba ku sauki ya kawo muku mafita." Ya ci gaba da yi wa karnukan nan addu'ayana shafa jikinsu. Duk wannan abu da ke faruwa, Abu Is'haka amintaccen Halifa na make bakin kofa yana leke da idanunsa yana kuma ji da kunnuwansa, yayi mamakin wannan abu matukar mamaki.


KU BIYO MU DON CIGABAN WANNAN LABARI
No comments:
Write Comments