Friday

Home Hattara! : "Yan ta'addar jihar zamfara sun fara kaura suna shiga wasu jahohi.
A ranar Alhamis dinnan ne da ta gabata, gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola, ya bukaci jami'an tsaro da sarakunan gargajiya da su lura sannan kuma su dakile duk wani shiri na 'yan ta'addar jihar Zamfara, wadanda suke yin kaura daga jihar suna komawa wasu jihohi.

zamfara killings, kashekashen zamfara

Hakan ya biyo bayan sanarwar da babban sakatarensa a fannin sadarwa ya fitar, Mista Adeniyi Adesina, bayan gwamnan ya yi magana a wurin wani taro, akan gudanar da tsarin tsaro, wanda sarakunan gargajiya, shugabannin hukumomin tsaro, kungiyoyin jama'a, 'yan siyasa, 'yan kasuwa da sauransu suka hallata a Osogbo.


Oyetola ya ce "ya zama wajibi a sanya matakan da za su magance matsalar 'yan ta'adda da ke faruwa a jihar Zamfara shigowa jihar Osun."
Gwamnan ya jaddada bukatar tabbatar da tsaro ta hanyar tattara bayanai, sannan sarakunan gargajiya su saka ido a yankunansu da kuma bukatar a fadakar da jami'an tsaro su sanya ido wurin dakile duk wani shiri na ta'addanci a jihar.

Gwamnan da kuma jami'an tsaro sun gargadi masu bada gidajen haya, akan bai wa mutane wadanda ba su da kyakkyawar masaniya a kansu.

KU KARANTA: A karon farko an yiwa wasu birai dashen kwakwalwar Dan-Adam.
"Idan ka bawa mutumin da baka san shi ba hayar gida, kuma muka gano cewa dan ta'adda ne, to duk abinda ya biyo baya kai ka jawowa kan ka," in ji Oyetola.

Ya bukaci sarakunan gargajiya da su yi aiki tukuru, domin masu hakar ma'adanai suna nan suna yawo a wasu yankuna na cikin jihar.

Gwamnatin tarayya ta hana hakar ma'adanai a jihar Zamfara, bayan ta samu bayanan cewa 'yan ta'addar jihar su na da alaka da masu hakar ma'adanai wadanda ba su da lasisi.

SOURCE LEGIT.NG
No comments:
Write Comments