Monday

Home Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun budewa sabon gwamnan Zamfara wuta
A jiya Lahadi ne, wasu yan bindiga sun budewa motar sabon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, wuta yayinda yake hanyarsa na jajintawa wadanda suka rasa yan uwansu a wani hari da aka kai karamar hukumar Gusau, Premium Times ta bada rahoto.

Masu Idanuwan shaida sun bayyana cewa an budewa motar gwamnan wuta ne da yammacin Lahadi a hanyar garin Lilo.

Majiya ya bayyana cewa Yayinda suka kai harin, yan bindigan sun yi amfani da damar tsayin ciyayi inda suka bude masa wuta.

Ya kara da cewa zuwa yanzu ba'a san yawan wadanda aka rasa ko suka jikkata ba, saboda masu tsaron gwamnan sun yi batakashi da yan bindigan.

KU KARANTA: Yadda Wani dalibi ya kashe kansa a dalilin sabani da budurwarsa.

A rahoton da muka kawo da saifyar yau, mai magana da yawun Sabon gwamnan jahar Zamfara, Bello Matawalle ya bayyaa cewa gwamnan ya jagoranci ayarin jami’an rundunonin tsaro inda suka fantsama cikin dazukan kauyen Wonaka dake garin Gusau da nufin farautar miyagun yan bindiga da suka addabi al’ummar yankin.

Kaakakin, Yusuf Idris ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuni, inda yace gwamnan ya samu rakiyar mataimakin gwamnan jahar, Mahadi Aliyu Gusau, da sauran kwamandojin rundunar tsaro, inda suka fatattaki yan bindigan.

A ranar Asabar, Akalla mutane 8 sun rasa rayukansu yayinda 18 suka jikkata harin da aka kai garin Lilo.

Har ilayau, jihar Zamfara da wasu jihohi basu gushe suna fuskantar barazana daga wajen yan bindiga ba.

SOURCE LEGIT.NG


No comments:
Write Comments