Friday

Home › › HIKAYAR BIRNIN DUWATSU 03
Yayin nan ya ja shi kasa ya kai ga gadon nan ya daure shi ga bigirensa. Ya kwance kare na biyu, ya aikata bugu gare shi kamar yadda ya yi wa na fari. Daga nan sai ya ciro adiko ya riga goge musu jikinsu yana ba su hakuri yana cewa, "Kada ku rike ni da wannan abu, ba da son raina na aikata muku shi ba. Allah ya ba ku sauki ya kawo muku mafita." Ya ci gaba da yi wa karnukan nan addu'ayana shafa jikinsu. Duk wannan abu da ke faruwa, Abu Is'haka amintaccen Halifa na make bakin kofa yana leke da idanunsa yana kuma ji da kunnuwansa, yayi mamakin wannan abu matukar mamaki.



CIGABA....



Duk wannan abu da ke faruwa, Abu Is'haka amintaccen Halifa na make bakin kofa yana leke da idanunsa yana kuma ji da kunnuwansa, yayi mamakin wannan abu matukar mamaki. Bayan karnuka sun farfado, sai Abdullahi ya jawo kabakin nan ya rika ba su abinci da hannunsa suna ci har suka koshi. Ya goge musu bakuna. Ya dauko kaskon ruwa ya shayar da su. Daga nan sai ya dauki kabaki da bulala ya riki shama'a ya nufi kofar fita. Abu Is'haka ya yi sauri ya koma bisa gadonsa, ba tare da Abdullahi ya gan shi ko ya ji motsinsa ba, ya kwanta kamar yana barci. Abdullahi ya mayar da kabaki da kaskon ruwa a cikin taska, ya dawo cikin soro ya mayar da bulala cikin akwati, ya kwance damara, sa'annan ya kwanta bisa gadonsa. Abu Is'haka kuwa yana kwance ya kasa barci saboda tunanin wannan abu da ya gani, sai mamaki ke cin sa. Ya rika cewa a cikin ransa, "Ina mamakin dalilin wannan abu da na gani." Ba shi ya daina tunani da al'ajabi ba sai da gari ya waye. Yayin nan suka tashi suka sallaci sallar asubahi suka karyakumallo suka sha abin sha, sa'annan suka shirya suka fita fada. Zuciyar Abu Is'haka ta cika da tunanin al'amarin da ya gani mai ban mamaki, har aka yi fadanci aka tashi hankalinsa ba ya tare da shi, kuma bai tambayi Abdullahi dalilin wannan abu ba. A dare na biyu Abu Is'haka ya sake bin Abdullahi a baya, ya ga ya aikata wa karnukan nan abin da ya yi musu a daren jiya. Ya buge su da bulala, ya shafe musu jiki yana ba su hakuri, sa'annan ya ba su abinci da abin sha. Haka kuma a dare na uku ya aikata musu. A rana ta hudu sai Abdullahi ya kawo haraji ya ba Abu Is'haka tare da tsaraba mai yawa, suka yi ban kwana ya tafi, ba tare da ya tambayi sababin bugun karnuka ba, ya bar abin a cikin ransa. Kwanci tashi har ya iso birnin Bagadaza, ya ba Halifa haraji wanda ya tambayi dalilin jinkirin kawo shi. Abu Is'haka ya amsa masa, "Ya Shugaban Muminai, ko da na isa na tarar da ya gama tattara harajin har ya yi nufin aikowa da shi, da a ce ma na kara kwana daya ban isa ba, da na hadu da manzanninsa a hanya.Amma ya Shugaban Muminai, na ga wani abu da ya daure mini kai, ya sanya ni cikin tunani da al'ajabi mai girma, tare da Abdullahi dan Falilu. Ban taba ganin wannan abu ko jin labarinsa ba tun da nake." "Wane abu ne wannan da ka gani mai ban mamaki, ya Abu Is'haka?" Halifa ya tambaya. Abu Is'haka ya amsa, "Na ga abu kaza da kaza." Ya kwashe labarin abin da ya ga Sarkin Basara na aikata wa karnuka cikin dare ya fada masa. Ya kara da cewa, "Haka na ga yana yi tsawon dare uku da na kwana tare da shi. Da farko sai ya bugi karnukan sai sun suma, sa'annan ya rika shafe jikinsu da kyalle yana rarrashi. Idan suka farfado sai ya ciyar da su abinci ya shayar da su ruwa. Ni kuwa ina make daga wajen dakin ina kallonsa, bai taba lura da ni ba." Halifa ya tambaye shi, "Ka tambaye shi dalilin wannan al'amari?" Abu Is'haka ya amsa, "A'a, Allah ya ja zamanin Sarkin Musulmi." Halifa ya cika da mamaki. Ya dubi Abu Is'haka ya ce, "Maza ka koma Basara ka taho mini da Abdullahi dan Falilu da karnukan nan biyu." Abu Is'haka ya sunkuyar da kai kasa ya ce, "Ya shugaban Muminai, ka dora mini aiki mai nauyi. Abdullahi ya girmamani ya kuma yi mini alheri mai yawa lokacin da na sauka gare shi. Wannan abu da na gani sirri ne gare shi da ba ya son kowa ya sani. Yanzu da wace fuska zan tinkare shi har na yi masa maganar karnukan nan duk da irin alherin da ya yi mini, Wallahi ina jin kunyar yin haka. Da zai yiwu, sai Sarkin Musulmi ya aika wani manzo da takarda yana umurtar Abdullahi ya zo tare da karnukan." Halifa ya yi murmushi ya ce, "Idan na aika wani zai iya musantawa ya ce, 'ni ba ni da wasu karnuka,' amma idan kai ka tafi ka ce masa, 'na gan su da idona' ba shi da ikon musantawa. Don haka dole kai za ka tafi ka zo mini da shi da karnukan nan, idan kuwa ba haka ba ina yanka ka." Abu Is'haka ya ce, "Na ji, na dauka, ya Sarkin Musulmi, Allah ya agaje mu. Da ma an ce harshe shi ke yanka wuya. Laifina ne da na gaya maka wannan labari, amma ina so ka rubuta mini takarda da hannunka wadda zan ba shi."



A CIGABA DA KASANCEWA DAMU DON CIGABAN HIKAYAR
No comments:
Write Comments