Sunday

Home KUN SAN ABIN DA YA FARU A KANNYWOOD A SHEKARAT DA MUKAYI BANKWANA DA ITA WATO 2016 ???
Shekarar 2016 na cikin shekarun da masu ruwa da tsaki a fina-finan Hausa, wato Kannywood ba za su manta da ita ba.

Abubuwa da dama sun faru a shekarar — masu dadi da marasa dadi — wadanda suka yi tasiri kan yadda ake tafiyar da wannan babbar harka.
Tun a farkon shekarar ne, wato a watan Fabrairu, Kannywood ta soma samun babban gibi sakamakon mutuwar fitacciyar jarumar nan Aisha Dankano.
Aisha — wacce aka fi sani da Sima - ta yi fice wajen amfani da kalmomi masu cike da hikima da kuma ban-dariya a fina-finan Hausa, wadanda da wuya a samu wanda ko wadda za ta maye gurbinta a wannan bangare.

Al'amura sun ci gaba da tafiya kamar yadda suka kamata a Kannywood, inda aka rika sa ran fitar da manya manyan fina-finai kamar su Basaja Gidan Yari, har watan Yuni lokacin da batun gina katafariyar alkaryar fina-finai ya taso.
A wancan lokacin, shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Isma'ila Na'abba Afakallah, ya shaida min cewa alkaryar za ta kasance ta farko a Najeriya, yana mai cewa masu shirya fina-finai daga kowacce kusurwa ta duniya za su iya zuwa Kano domin yin amfani da ita.
A cewarsa "Za a kashe sama da Naira biliyan uku wajen gina alkaryar, kuma ana sa ran fiye da mutum 10,000 za su samu aiki idan aka kammala aikin."
Sai dai nan da nan wannan batu ya jawo ce-ce-ku-ce kuma muhawarar da aka rika tafkawa a shafukan sada zumunta na zamani a kan dacewa ko rashin dacewar gina alkaryar da kuma caccakar da shirin ya sha a wajen wasu Malamai sun tilasta wa gwamnatin tarayya soke shi.

'Mu ba ɗan luwaɗi ba ne'

Tun bayan da gwamnatin tarayya ta soke shirin gina alkaryar fina-finai ne dai aka rika yin musayar yawu a tsakanin wasu 'yan fim da malamai, inda aka ambato wasu malaman na cewa wasu 'yan fim din 'yan luwadi ne, yayin da wasu 'yan fim din suka rika yin gugar-zana ga malaman.
Sai dai da alama batun zargin luwadin da aka yi wa 'yan Kannywood din ya shiga kunnen jama'a, lamarin da ya harzuka 'yan fim din.
A wata hira da fitaccen jarumi Adam A. Zango ya yi da gidan talabijin na DITV da ke Kaduna, ya musanta zargin yin luwadi.
Jarumin ya dafa Al-Qur'ani, sannan ya sha rantsuwa cewa bai taba yin luwadi ba, kuma shi ma ba a taba yi da shi ba, yana mai cewa idan har kalamansa babu gaskiya a ciki, Allah "ya halaka ni".
Shi ma jarumi Baban Chinedu, a wani bidiyo da ya fitar, ya musanta zargin.
Ya kara da cewa, "Wallahil azimun! Wallahil azimun ni ban taba luwadi ba, kuma ba a taba luwadi da ni ba!"
Abokin aikinsa ma, Mustapha Badamasi, wanda aka fi sani da Naburaska, ya caccaki mutanen da suke yi musu kazafi, yana mai cewa nan gaba kadan zai fito da shaidun da za su tozarta mutanen.

'Rahama Sadau ta tsokano gidan runa'


Masu nazari a harkar fina-finan Hausa sun yi ittifaki cewa rabon da Kannywood ta shiga rikici kamar wanda Rahama Sadau ta janyo mata tun bayan faifan bidiyon tsaraicin Maryam Hiyana da ya fita a shekarun baya.
A watan Satumba ne Rahama ta fito a waka salon hip hop mai suna I Love You tare da mawakin nan Classiq, wacce ke da tsawon minti hudu da dakika 19.
A wurare da dama an nuna ta tana jingina a jikin Classiq, lamarin da ya jawo zazzafar muhawara a tsakanin masu ruwa da tsaki na Kannywood da ma al'uma.
Hakan dai ya sa kungiyar masu harkar shirya fina-finan Hausa, MOPPAN, ta sanar da korar ta daga Kannywood.
Jarumar ta nemi gafara kan wannan batu kodayake ta ce ba zai yiwu ta yi aiki ba tare da "na taɓa wani ba".

'Yan Kannywood ke 'rige-rigen'

kafa gidauniya
Wani abu da ba za a manta da shi a wannan shekarar game da 'yan Kannywood ba shi ne yadda wasunsu suka mayar da hankali wajen taimakawa jama'a ta hanyar kafa gidauniya.
Jarumai irinsu Adam A. Zango da Nafisa Abdullahi da Hadiza Gabon sun kafa gidauniyoyi domin abin da Gabon ta bayyana da cewa "nuna godiya ga Allah bisa baiwar da ya yi mana, sannan mu nunawa marasa karfi cewa Allah yana tare da su."
Ita dai wannan jaruma ta bayar da tallafi sau da dama ga 'yan gudun hijirar da suka bar gidajensu sakamakon hare-haren kungiyar Boko Haram, wadanda yanzu haka suke sansanonin 'yan gudun hijira.
Baya ga haka, tana taimaka wa daliban kananan makarantu da litattafai da sauran kayan koyon karatu.
Shi ma a nasa bangaren, Adam A Zango ya kafa wata gidauniya mai suna Zango Intervention Initiative.
A cewar jarumin, gidauniyar za ta rika bayar da taimako ga marasa galihu da marasa lafiya da 'yan gudun hijira da marayu da zawarawa.
Zango ya ce zai samu kudin gudanar da gidauniyar ne ta hanyar shirya bukukuwan rawa a dukkan jihohin Najeriya wanda zai soma a watan Janairu mai zuwa.
Ita ma Nafisa Abdullahi ta kafa irin wannan gidauniya mai suna The Love Laugh Foundation, wacce ta ce za ta mayar da hankali ne kan nuna kauna da tallafi ga marasa galihu da mata da marayu da 'yan gudun hijira.
Masana abubuwan da ke faruwa a Kannywood sun yi san-barka ga wannan kokari da jaruman ke yi na taimaka wa al'uma.
Malam Ibrahim Sheme, wanda ya dade yana tsokaci kan Kanyywood, ya ce matakin zai inganta dangantakar da ke tsakanin jaruman da al'umar da ke yi musu kallo a matsayin masu wargaza tarbiyya.
Ya kara da cewa, "Wannan mataki yana da kyau amma ina ganin ba shi da tsari. Ya kamata jarumai kamar goma wadanda ke da irin wannan aniya su hada kungiya da za ta rika aiwatar da irin wannan shiri, ba kowa ya yi gaban kansa ba."
A yayin da muke bankwana da shekarar 2016 kuma muke shirin shiga sabuwar shekara, babu makawa cewa harkokin da ake gudanarwa a Kannywood za su ci gaba da jan hankalin jama'a da kuma yin tasiri a rayuwarsu.
No comments:
Write Comments