Saturday

Home › › Sai likitoci sun amince zan dawo :: BUHARI
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba zai dawo kasar ba har sai likitocinsa sun ce ya dawo kamar yadda aka wallafa a wasikar da ya aika wa Majalisa don tsawaita hutunsa.



Shugaba Buhari da yanzu haka ke jinya a birnin Landan ya sanar da hakan ne a cikin wata wasika da ya aika wa Majalisar Dattijan kasar a kwanakin baya bayan nan inda a ciki ya bukaci Karin hutun wasu kwanaki.

Buhari ya soma daukar hutun kwanaki goma kafin daga bisani ya kuma aika wasika gaban Majalisar kasar na neman Karin hutun don ci gaba da jinya al’amarin da ya sa wasu daga cikin al’ummar kasar ke rade-radin cewar shugaban ya mutu.



@facebook/HAUSAPOST28
No comments:
Write Comments