Wasu daga cikin sojojin Najeriya da ke ayyukan tabbatar da tsaro
A wani al'amari mai daure kai, bam ya tashi da wasu mutane da dama a wani kauye a Jahar Naija. Cikin wadanda abin ya rutsa da su har da wani soja da ake jin shi ke dauke da bam din.
Hukumomi a jahar Naija ta arewacin Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane hudu, ciki har da wani soja, a wani tashin bam din da ya auku a wani kauye mai suna Beri da ke Karamar Hukumar Mariga.
Majiyoyi sun ce sojan mai suna Tanko Damina, shi ne ya taho da bam din daga Maiduguri, inda ya ke aikin tsaro. Majiyoyin sun ce Damina, wanda hutu ya kawo shi gida Beri, ya na dauke da bam din lokacin da ya ratsa cikin kasuwa, inda bam din ya tashi ya hallaka shi da wasu ‘yan mata farar hula uku, baya ga wasu mutanen kuma biyar da su ka jikkata.
Shugaban Karamar Hukumar Mariga ‘Barista’ Abdulmalik Sarkin Daji, wanda ya je asibitin don jajanta ma wadanda abin ya rutsa da su, ya ce, ya ce tuni jami’an tsaro su ka shiga al’amarin. Y ace mutanen garin da kuma iyayen sojan sun tabbatar cewa lallai sojan gwamnati ne.
Daya daga cikin wadanda su ka jikkata din mai suna Muhammadu Danmajaja Beri, ya ce ya fito daga dakin cin abinci kawai sai ya gan shi a kasa tare da sauran, ciki har da ‘yan matan da su ka rasu.
Kakakin Hukumar ‘Yansandan Jahar Naija DSP Elkana ya tabbatar ma wakilinmu Mustapha Nasiru Batsari da aukuwan al’amarin.
No comments:
Write Comments