Thursday

Home › › BUHARI ZAI DAWO GIDA NIGERIA RANAR ASABAR

Alamu na cigaba da nuna yiwuwar
dawowar shugaban kasa Muhammadu
Buhari gida Najeriya a ranar Asabar 11 ga
watan Feburairu daga hutun daya tafi a
kasar Ingila.
Buhari a Landan
Wata majiya kakkarfa ta cikin gida ta
shaida ma jaridar Leadership haka.
Majiyar tace, “idan dai ba an canza
shawara ba, muna sa ran dawowar
shugaban kasa a cikin kwanakin
karshen mako, musamman ranar
Asabar.





image


Jaridar ta binciko cewar a ranar Talatar
data gaba ne shugaba Buhari ya soke
shirin gudanar da hira ta musamman ga
wata gidan jarida dake kasar waje,
amma ana tsammanin zai yi hirar da
wata jarida ta daban kafin satin nan ya
kare.

Wata majiyar ta daban ta shaida mana
cewar: “A yanzu haka shugaba Buhari
ya kammala shirya jakunkunansa don
shirin daowa gida ranar Lahadi, amma
sai likitocinsa suka shawarce shi daya
dakata har sai an fitar da sakamakon
gwaje gwajen da aka yi masa.

“Ina tabbatar muku shugaba kasa zai
iya cigaba da zama a ksar Landan
sakamakon likitocins sun matsa masa
akan lallai ya dakata da tafiyarsa, amma
gaba daya hankalinsa na gida Najeriya.”
Dangane da jita jitan da ake yadawa na
cewa shugaban na cikin halin rai
fakwai-mutu fa kwai kuwa, majiyar ta
ce, “kana mamakin jin haka daga
mutanen mu ne? da ace
shuwagabanninmu na baya ne suka fita
ba tare da sanar da majalisa ba, da za
zaka ji wannan surutan ba. Amma
wannan shugaban namu ya dage akan
lallai sai ya bi doka, kuma ba wannan
bane karo na farko da ya fara fita kasar
waje ai.”


Jaridar Leadership ta ruwaito kaakakin
shugaban kasa Femi Adesina yana fadin
cewar nan bada dadewa bane shugaba
Buhari zai dawo.

Idan za’a iya tunawa, a ranar Lahadin
data gabata ne shugaba Buhari ya aika
ma majalisa da takardan inda a ciki
yake sanar dasu zai tsawaita zamansa a
kasar Ingila don ya jira ya amshi
sakamakon gwaje gwajen da aka yi
masa, kamar yadda likitocinsa suka
bashi shawara.

A wani labarin kuma, ministan watsa
labarai da al’adun gargajiya, Alh Lai
Muhammed ya bayyana a jiya cewar
abin dariya ace wasu su dinga kamanta
tafiyar shugaba Buhari da na tsohon
shugaba Yar’adua.

Muhammed ya bayyana haka ne bayan
taron majalisar zartarwa wanda
mataimakin shugaban kasa Farfesa
Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar
shugaban kasa, wannan batu na
Muhammed yazo ne kwanaki biyu
bayan Osinbajo ya jaddada cewar
shugaba Buhari ne kadai keda daman
fitar da matsayin lafiyarsa.

Da aka tambaye shi ko shugaba Buhari
na cikin koshin lafiya, Lai Muhammed
yace “ina tabbatar muku cewar shugaba
Buhari na cikin cikakken koshin lafiya,
babu wata tantama. Amma kuna ganin
shugaba Buhari zai shiga cikin halin
rashin lafiya kuma ace muna nan muna
gudanar da ayyukan mu kamar ba
komai?

Wasu sun zarge ni akan na bukaci a
dinga fitar da bayanin rashin lafiyar
Umaru Yar’adua a duk sa’a, toh ina so
in fada musu, babu wata
kamanceceniya ko kada tsakanin
shuwagabannin biyu, don kuwa Buhari
ba a asibiti yake ba, lafiyarsa kalau.

Da aka sake tambayarsa kowa ya dace
shugaba Buhari yayi tafiya alhalin ana
cikin halin matsin tattalin arziki? Sai
yace “sosai ma kuwa, shin shugaba
Obama ba yaje hutu ba? Idan ya zama
dole sai shugaban kasa ya tafi hutu, dole
ne ya tafi hutu, kasan yawan ministocin
da suka tafi hutu a shekarar nan?

@facebook/hausapost28
No comments:
Write Comments