Thursday

Home › › Jami`an tsaron Najeriya na fuskantar kalubalen samun hadin kan jama`a.
image


Rundunar sojojin ruwan tarayyar Nigeriya ta kaddamar da wani shirin dakile barazanar tsaron da ake fuskanta a yankin Niger Delta mai arizikin man fetur dake kudancin kasar.

Rundunar sojin ta yiwa shirin taken `operation tsaron teku`, domin yin fito na fito da bata garin dake fasa bututu, garkuwa da mutane da duk wani nau’in tashin hankali a yankin.

To sai dai babban kalu balen da ke fuskanta shi ne yadda ba a cika samun al’umma na tallafawa jami’an tsaro wajen fallasa bata garin ba, a yayinda wasu ke zargin fallasa su, idan sun bada sirrin.
Yayinda yake zantawa da sashin hausa na RFI Dr Abdullahi Yalwa shugaban sashin nazarin muggan dabi’u, da kuma dakile yaduwarsu na kwalejin kimiya da kere kere na Tatari Ali dake jihar Bauchi yace fargabar fallasa ba shi ne dalilin rashin bawa jami`an tsaro hadin kai don magance barazanar tsaro ba.

Dr Yalwa ya ce babban dalili shi ne rashin kishin kasa a tsakanin wasu daga cikin al`umma, sai kuma sankai wajen zagon kasa ga gwamnati saboda rashin goyon bayan da ake bata.

A cewar sa tallafawa jami`an tsaro hakki ne na kowane dan kasa, wanda kuma ba alfarma ba.
Dr Yalwa ya buga misali da yankin arewa maso gabashin Najeriya inda ya ce kowa yaga yadda jama`ar gari suka tashi tsaye wajen magance barazanar tsaron Boko Haram, ta hanyar kafa rundunar sa kai, da aka fi sani da Civilian JTF, da hadin gwiwar jami`an tsaron Najeriya.

Dan haka, a cewarsa idan har al`ummar arewa maso gabashin Najeriya zasu iya wannan yunkuri, ya zama tilas al`ummar yankin Niger Delta su bada tasu gudunmawar wajen tallafawa jami`an tsaro.

@facebook/hausapost28
No comments:
Write Comments