Wani malamin makarantar sekandare a
jihar Legas ya shiga hannun jim'an tsaro a
yayin da ya damfare dalibansa.
Jami’an tsaro su cafke wani malamin
koyarwa a makarantar sekandare,
Abayomi Abdul yayin da ya damfare
wasu dalibansa yawan kudi 500,000.
Malamin mai shekara 49 da haihuwa
wanda aka kawo a gaban wani kotu
majistare a Ikeja a ranar Alhamis, 23 ga
watan Fabrairu, bisa zargin karba kudi
hannun wasu dalibai 14.
A cewar kamfanin dillancin labarai na
Nijeriya, Abdul wanda ya ke koyarwa a
wani makarantar sekadare “Mercy
Secondary School” a jihar Legas ya
damfare dalibai a kan zai yi masu
rejistan jarrabawa.
Mai gabatar da kararraki, Mike Unah,
ya shaida wa kotun cewa wanda ake
zargin ya aikata laifukan a watan Mayu
2014 da ta gabata. Ya ce: "Malamin ba
shi da niyyar rijista dalibai kamar
yadda ya yi alkawari."
Majistare, A.O. Gbajumo ya dakatad da
shari’a zuwa Litinin, 6 ga watan Maris
domin cigaba da sauraren karan.
No comments:
Write Comments