Wani rikici da ya barke tsakanin kungiyoyi biyu na ‘yan tawayen Syria da ke dasawa da juna, ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 70 a cikin sa’oi 24. Kungiyoyin Fateh al Sham da kuma Jund al Aqsa da ke lardin Idlib sn samu Baraka ne a tsakaninsu, inda a can baya suka hada kai don yaki da dakarun gwamnatin shugaba Bashar Assad.
Kungiyar da ke sa ido kan Syria mai cibiya a Birtaniya ta ce, rikicin ya barke ne bayan Jund al Aqsa ta kai harin bam a shalkwatan Fateh al Sham, in da ta kashe mambobinta 9. Wannan na zuwa a yayin da ake kokarin shawo kan rikicin Syria a Kazakstan tsakanin bangaorrin ‘Yan tawayen da suka rarrabu da kuma bangaren gwamnatin Assad. A gobe Laraba ake sa ran gudanar da tattaunatawar a birnin Astana tsakanin wakilan ‘Yan tawaye da gwamnati karkashin jagorancin Iran da Rasha da kuma Turkiya.
@facebook/HAUSAPOST28




No comments:
Write Comments