Tuesday

Home Alamu sun nuna Za ayi Matsanancin Zafi a 2017



(Wasu Yara na sanyaya jikinsu daga zafin da ake makawa a
Koriya ta Kudu)

Binciken Majalisa Dinkin Duniya ya nuna cewar a bana za
a fuskanci matsanancin zafin kamar na bara da aka
bayyana mafi tsanani da aka taba fuskanta a duniya.

David Carlson, shugaban hukumar binciken yanayi ta
Majalisar ya ce ko da babu matsalar fari da aka yi wa
lakabi da El Nino wanda ta haifar da matsalar tsakanin
shekaru 4 zuwa 5 da suka gabata, shekarar 2017 na tafe
da wasu sauye sauye da ke kalubalantar sanin da suka yi
wa yanayin.

An dai wallafa wannan gargadi ne ranar talata a rahotan
hukumar na shekara shekara, wanda ya tabbatar da
cewar shekarar 2016 ita ce mafi zafi a tarihi.
Ma’aunin zafin ya kai 1.1 na Celsius fiye da na bara 0.06.
Rahoton ya ce gurbataccen iskan da ake fitarwa
musamman a kasashe masu manyan masana’antu ne
ke haifar da dumamar yanayin.
No comments:
Write Comments