Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa’i ya rubuta wasika
ga shugaba Muhammadu Buhari kwanaki inda ya
fada masa cewa akwai gyara a tafiyar. Sai dai yanzu
mun gano dalilin da ya Malam Nasir El-Rufa’i ya
rubuta wannan takarda
Kwanan nan aka samu labarin cewa Gwamnan
Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya rubuta wata
wasika ga shugaban kasa Muhammadu Buhari inda
yake kiran sa da yayi maza yayi wasu gyara a
mulkin sa, ciki dai ana bukata ya sallami wasu na
kusa da shi irin su Abba Kyari da Babachir Lawal.
Sai dai bincike da wata Jarida tayi an gano cewa
ashe shugaba Buhari ne da kan sa ya nemi Malam
Nasir El-Rufa’i ya rubuta wannan takarda a sa’ilin
da su ka hadu a Garin Daura lokacin bikin Sallah a
Satumban bara.
El-Rufa’i ya ziyarci Buhari da Sallah
Dama can an yi taro da Kungiyar Arewar nan ta
ACF inda suka nemi a fadawa Buhari cewa ya tsige
Sakataren Gwamnatin sa da kuma Shugaban
Ma’aikatan gidan Gwamnati. Haka kuma Gwamna
El-Rufa’i ya rubuta cikin takardar ta sa bayan
nazari.
Rahotannin sun nuna cewa wasu na kusa da
shugaban kasar ne su ka fito da takardar Duniya ta
gani domin a dauka cewa Gwamna El-Rufa’i yana yi
wa Shugaba Buhari zagon kasa ne. Wasu dai na
ganin cewa siyasar tana kadawa ta wajen Gwamnan
na Jihar Kaduna kuma suke kokari su taka masa
birki.
No comments:
Write Comments