Saturday

Home Amfanin Gishiri Guda 10 Musamman Ga 'Yan'uwa Mata.

sinadarin gishiri



Gishiri yana da amfani da yawa bayan zubawa a
cikin abinci, mutane da yawa sun zata amfanin
gishiri shi ne kawai a zuba a cikin miya, amma
ina, amfaninsa ya fi ga haka.



kwararru a fannin kiwon lafiya sun tabbatar cewa
baicin abin da muka sani na al’ada, wato amfanin
Gishiri cikin miya, hakikatan sun tabbatar cewa
Gishiri dai yana da dimbin sirruka da amfani ga
dan adam.



Ga wasu daga cikin amfanin sa:


  • 1. kowa ya san cewa idan Kyandir ya
    diga a waje, tilas zai manne da wajen, har sai an
    kankare shi da karfin tuwo, amma muddin ki ka
    jika Kyandir din ki na tsawon awa biyu ko uku, to
    da zaran kin kunna shi, yana ci, ko da zai diga a
    waje, ba zai kama ba. Za ki sha mamaki, domin
    da kin dan murje shi, zai fita, tamkar Kyandir bai
    taba diga wajen ba.



  • 2. Ina mata masu amfani da risho ko abin gashi
    irin na lantarki ko wanda ake amfani da Gas?
    Mafi yawan lokaci idan kina girki za ki ga ruwan
    girkin ko man gyada da ki ka yi suya da shi, ko
    dai wani abu da ki ka dafa a kan risho ya bata
    shi sosai, kafin kuma ki gama girkin ya bushe,
    don haka da rishonki ya fara baci sai ki barbada
    gishiri a wajen, da kin gama girki idan ya huce
    kina saka soso za ki ga ya fita. Haka ma za ki yi
    wa dukkanin ababen girkin ki.



  • 3. Idan kina tantaman kwai ko ya lalace ko yana
    da kyau, sai ki zuba gishiri karamin cokali biyu a
    cikin ruwa, ki kada, ki zuba kwan a ciki, idan
    yana da kyau za ki ga kwan ya yiwo sama yana
    yawo, idan kuma ya lalace ne kuma za ki ga ya
    yi kasa, sabanin abin da aka saba gani.



  • 4. Sosan wanke-wanke idan ba a tsaftace, shi sai
    ya zama waje ne da kwayoyin cuta suke
    dabdalarsu a ciki, don haka duk lokacin da ki ka
    gama wanke-wanke ki wanke sosan sosai, sai ki
    jika shi a cikin ruwan gishiri na awa daya ko
    biyu, kuma da zarar kin ga ya fara lalacewa ki
    yar da shi ki sayi wani, ba wani tsada ne da shi
    ba.



  • 5. Idan kin sayi tsintsiya kuma kina so ta dade
    miki, idan kin sayo tsintsiya kafin ki fara amfani
    da ita sai ki jika ta a cikin ruwan gishiri kafin ki
    fara amfani da ita.



  • 6. Idan zuma ta harbe ki, sai ki yi sauri ki zuba
    ruwan gishiri a wajen, yin hakan zai rage zafin
    harbin zumar, kuma wajen ba zai tashi ya yi ja
    ba.



  • 7. Amfani da ruwan gishiri mai dumi a lokacin da
    mutum yake fama da ciwon hakori da kuma
    ciwon makogaro yana kawo sauki, sai dai da
    kuna, idan kika daure kunar na wani lokaci ne,
    amma kafin jimawa za ki ga kin sami sauki.



  • 8. Ina masoya masu aikewa da junansu fulawa
    ko kuma masoya fulawa? Amma fulawar da nake
    nufi fulawar roba, na san ba kowa ne zai zauna
    ya goge fulawar ba idan ta yi datti ko kura,
    domin lungu da sakon da take da shi. Ki tsoma
    fulawar a cikin ruwan gishiri na ‘yan mintuna ki
    girgiza, dukkan dattin da ya ke jiki zai fita.



  • 9. Idan kina da madarar ruwa kuma tana saurin
    lalacewa, sai ki zuba gishiri dan kadan a ciki ki
    jijjiga ki rufe.



  • 10. Idan jini ya bata miki kaya, sai ki jika su a
    cikin ruwan gishiri ki wanke, sannan ki saka su a
    cikin ruwan dumi da Omo ki wanke. Haka kuma
    idan gumin hammata ya bata miki kaya, sai ki
    zuba gishiri a cikin ruwan dumi ki wanke kayan.
  • No comments:
    Write Comments