Cif Paulinu Akpeki wanda daman dan PDP
amma kuma sai ya koma APC a kwanakin baya
yanzu ya sake komawa PDP din.
Makomar jam'iyyar APC a jihar Delta tana rawa
da tangadi bayan wani babban jigon ta mai suna
Cif Paulinus Akpeki ya fice daga jam'iyyar ya
kuma koma jam'iyyar PDP da ke mulki a jihar.
Shi dai Paulinus Akpeki wani tsohon
kwamishinan jihar ne sannan babbar kusa a cikin
gwamnatin da ta gabata a jihar amma sai ya fice
daga jam'iyyar ta PDP a kwanakin baya kafin
daga bisani ya dawo jam'iyyar tasa ta asali.
An dai ruwaito cewa komawar tasa bata rasa
nasaba da dawowar tsohon gwamnan jihar
James Ibori.
No comments:
Write Comments