Thursday

Home Jawabin Jagoran Juyin Islama A Birnin Mashhad : iran







Jagoran juyin Islama na kasar Iran Ayatollah
sayyid Ali Khameni ya gabatar da jawabia gaban
dubban mutanen da suka taru a cikin hubbaren
Imam Ridha (AS) da ke birnin Mashhad, kamar
yadda ya saba yi a farkon kowace shekara ta
hijira shamsiyya.

Kamfanin dillancin labaran IRIB ya bayar da
rahoton cewa, a yayin jawabin nasa, jagora ya
jaddada muhimamncin mayar da hankali
matukan batun bunkasa ayyukan kere-keren
kamfanonin cikin gida, da kuma tabbatar da
samar da guraben ayyuka ga matasa, domin
bunkasa harkokin tattalin arzikin kasar daga
cikin gida.

Ya ce a kowane lokaci makiya suna amfani da
makamin tattalin arziki ne da nufin raunana
kasar Iran, duk kuwa da cewa bisa himmar
masana da sauran ma'akata masu kwazo, da
kuma taimakon Allah madaukkin sarki,a cikin
tsawon shekaru 37 na juyin Islama, makiya ba
su iya cimma wannan buri nasu ba a kan
jamhuriyar muslunci, a maimakon hakan a
kullum tattalin arzikin kasar na ci gaba da
bunkasa a matsayi na kasa da kasa.

Jagoran ya ci gaba da cewa a bangaren
ayyukan tsaro hakika an samu gagarumin ci
gaba, wanda da taimakon Allah madaukakin
sarki an cimma nasarori masu tarin yawa
bangarori daban-daban na ayyukan tsaro.
Dangane batun zabuka kuwa, jagoran ya ce
babban abin bukata shi ne al'umma su fito
kwansu da kwarkwatarsu a ranar zabe, domin su
zabi abin da su gamsu da shi, wanda shi ne
hakikanin 'yanci da adalci wanda ke tsorata
makiya dangane da damfaruwar al'umma da
juyin Islama.
No comments:
Write Comments