Friday

Home Buhari ya umarci Osinbajo ya cigaba rikon kwarya, yana bukatan hutawa kadan : Bayan Dawowarsa Daga kasar London A yau Juma'a 10-03-2017




Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar ya gaji sakamakon zaman jirgi da yayi daga kasar Birtaniya zuwa Najeriya, don haka mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ya cigaba da rikon kwarya, har sai y agama hutawa
Jaridar The Sun ne ta ruwaito labarin, inda tace shugaban kasa Buhari ya bayyana haka ne a lokacin dayake ganawa da majalisar ministocinsa, da kafatanin shuwagabannin hukumomi.
Yanzun nan: Buhari ya umarci Osinbajo ya cigaba rikon kwarya, yana bukatan hutawa kadan
Cikin wadanda suka halarcin zaman majalisar zartarwar sun hada da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, da gwamnan jihar Zamfara, Abdul Aziz Yari, kuma an gudanar da ganawar ne a boye.


A yayin ganawar, shugaba Buhari ya gode ma yan Najeriya da suka yi masa addu’an samun sauki da fata alheri, kuma ya tabbatar musu da cewa a yanzu ya samu sauki.
Buhari yace “ Koma dai menene, ina yi ma yan Najeriya godiya.”
Buhari yace yana sane da tsadar duba lafiyarsa a kasar waje, amma dai yace ya samu kulawar data dace kuma yadda ya kamata.
Da safiyar jum’a 10 ga watan Maris ne dai shugaba Buhari ya sauka Najeriya a filin sauka da tashin jirage na barikin sojojin sama dake jihar Kaduna, da misalin karfe 7:40. Inda ya garzaya ki tsaye zuwa fadar shugaban kasa da misalin karfe 8:37 na safe.
No comments:
Write Comments