Friday

Home "Zan kara komawa nan bada dewaba don kara duba lafiyata" : inji shugaba buhari



Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo daga kasar waje a ranar juma’a 10 ga watan Feburairu bayan kwashe kwanaki 50 ana duba lafiyarsa a kasar Birtaniya.

Sai dai a cikin jawabin da shugaban yayi a fadar gwamnati, yace akwai bukatar ya sake komawa can kasar Birtaniyan nan bada dadewa ba don a kara duba lafiyarsa.


KARANTA WANNAN :- Hukumar INEC ta Bayyana Ranakun zaben 2019



Shugaban ya bayyana haka ne a cikin jawabin dayayi inda yace “Ina matukar godiya ga yan Najeriya, musulmai da Kirista wadanda suka yi min addu’ar samun sauki da fatan alheri. Wannan wata manuniya ce dake nuna cewar duk da halin matsin da ake ciki, yan Najeriya suna baiwa gwamnati goyon baya don cimma burinta .

“Hanya mafi dacewa da zan bi in gode muku itace in dage wajen yi muku hidima, kare muradunkun tare da rike amanar da kuka bani hannu biyu biyu. Nagode muku sosai.

“Ina samun sauki yanzu ba kamar da ba, amma wata kila in sake komawa don a kara duba ni a cikin yan satuttuka masu zuwa” inji shugaba Buhari.

A nasa jawabin, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo yace ya gode ma Allah daya dawo da shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin koshin lafiya.


















No comments:
Write Comments