Majalisar Dattijai ta umurci shugaban hukumar kwastam Hameed Ali daya zo gabanta domin amsa tambayoyi ranar Laraba mai zuwa.
Majalisar ta umurceshi da ya ya tabbata ya sanya kayan aikin san a kwastam ba kayan gida ba idan zai zo din.
Majalisar ta sanar da hakanne a zamanta da tayi a zauren majalisar ranar Alhamis din da ta gabata.
Sanata Dino Melaye(APC Kogi) wanda shine ya jagoranci muhawaran ya karanta hujjujinsa wanda yace ya samo daga jaridar Sun kuma kamar yadda jaridar ta rubuta ta nuna cewa Hameed Ali ya ki bin umurnin majalisar na a daina yi wa motoci rajista da ita hukumar kwastam din takeyi.
Sanata Dino Melaye yace Hameed Ali ya ki bin umarnin da majalisar ta bashi a zamanta na ranar Talata duk da cewa shugaban hukumar kwastam din yace dokar hukumar bata hana su yin hakan ba.
Da suke tofa albarkacin bakinsu a mahawaran Sanata Kabiru Marafa (APC-Zamfara), Sanata Emmanuel Bwacha (PDP-Taraba), Sanata Aliyu Wamako (APC-Sokoto) da Sanata Solomon Olamilekan (APC-Lagos) duk sun goyi bayan cewa Hameed Ali ya bayyana a gaban majalisar.
Mataimakin shgaban majalisar Dattawan Ik Ekewemadu wanda shine ya jagoranci zaman majalisar ya amince da korafin ‘yan majalisar kuma y ace lallai hameed Ali ya bayyana a gaban majalisar.
KARANTA WANNAN :- Dokar kayyade aure ta Allah ce ba sarkin Kano Ba - Shugaban Izala.
Daga karshe shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa Ahmed Lawan ya shawarci ‘yan majalisan da su yi taka tsantsan da irin rahotanin da suke karantawa a jarida sannan domin tabbatar da sahihancinsu don yin amfani dasu a matsayin hujja a akan abin da zasu tattauna a majalisar.
Ya kuma ce duk wanda majalisar ta bukata da ya zo gabanta ya zama masa dole ya zo.
No comments:
Write Comments