Saturday

Home KARANTA : Wandon wani Lauya ya kama da wuta ana tsaka da shari'a.



Wandon lauyan mai kare wani mutum da ake ƙara, ya kama da wuta a gaban kotun Florida ana tsaka da shari'ar ta da gobara.

Shaidu sun ce aljihun Stephen Gutierrez ya fara bal-bal da hayaƙi lokacin da ya tsaya gaban kotu, don yi wa masu taya alƙali yanke hukunci jawabi a ranar Laraba
Tarin zububai? Wandon lauya ya kama wuta tun a duniya


Daga nan sai lauyan ya fita a guje, kuma ya dawo kotun da ƙonannen aljihu ba tare da jin rauni ba, inda ya zargi baturin taba sigarinsa ta lantarki, a cewar Miami Herald.


KARANTA WANNAN :- Dokar kayyade aure ta Allah ce ba sarkin Kano Ba - Shugaban Izala.



Mr Gutierrez, wanda ke mujadala kan cewa motar mutumin da yake karewa haka kawai take kamawa da wuta, ba wani hatsabibanci ne ya shirya ba.
'Yan sanda da masu shigar da ƙara sun gudanar da bincike kan lamarin, inda jaridar ta ruwaito cewa har jami'an tsaro sun ƙwace baturan sigarin lantarki da suka toye a matsayin shaida.

Lauyan na wakiltar Claudy Charles, wanda ake tuhuma a kan cinna wa motarsa wuta da gangan.

Daga bisani dai kotun ta samu Claudy Charles da laifin tada gobara.



No comments:
Write Comments