hakika Rayuwa da mutuwa a hannun Allah
suke. Babu wanda ya san lokacin da zai
cika. Idan muka waye gari ko muka
kwanta bacci, ko shakka babu munada
shirin yi wani abun domin cigaban
rayuwa. Duk da cewa mun san wata
rana zamu cika ba tareda karashe aikin
da muke niyyan yi ba.
Matukin jirgin sama ya rasu yana tukin jirgi SV
1734 a kasar Saudiyya
A yau zamuyi Magana akan wani
direban jirgin kaar saudiyya wanda ya
rasu yana tukin jirgin sama. A ranan, 1
ga watan Maris, jirgi mai lamba Flight
SV 1734 ta tashi daga filin jirgin saman
Bisha zuwa birnin Riyadh. Komai na
tafiya daidai kawai sai wani abin
mamaki da ban tsoro ya faru.
Direban jirgin mai suna Waleed Al-
Mohammed, wanda an tabbatar yanada
lafiya da samu ciwon zuciya. Anyi
iyakan kokari amma lokaci yayi. Amma
da gaggawa suna sararin samaniya,
mataimakinsa ya cigaba da tukin jirgin
har suka sauka a babban filin jirgin
saman King Khaled dake birnin Riyadh.
Allah ya jikanshi da rahma, mu ma idan
lokacinmu yayi ya sa mu cika da kyau
da imani.
No comments:
Write Comments