Michael Barnes ya girma a matsayin mabiyi
addinin kirista a Alexandria, Louisiana. Ya
shiga aikin soja yana da mai shekara 23.
Sojan kasar Amurka ya musulunta bayan wata
mukabala
Lokacin da aka turasu kasar Jamus
domin aiki, ya hadu da wani Sojan
Amurka musulmi wanda ya kasance
yana ma mutane da’awah akan
musulunci.
Ashe wannan abu na baiwa Michael
Barnes haushi. Wata rana sai ya
kalubalancesa cikin jama’a har suka
fara muhawara akan musulunci da
Kiristanci. Sauran sojin 30 sun shaida
mukabalan.
Ba tare bayani filla-filla akan
mukabalan da sukayi ba Michael Barnes
yace : “ Soja musulmin yayi mini bayani
filla-filla game da addininsa tamkar ya
sihirce ni, yayi mini bayanin musulunci
fiye da abinda nike tsammani. Na
kasance ina tunanin cewa ina rike da
gaskiya amma yau nayi mamakin abinda
na saurara."
Bayan an kammala mukabalan ,
Michael Barnes ya fara karatu akan
addinin musulunci. Kulli yaumin sai ya
karanta Alkur’ani da Bible. Bayan
shekaru biyu na bincikensa sai ya furta
Kalmar shahada kuma ya canza
sunansa zuwa Khallid Shabazz.
No comments:
Write Comments