Mutane 4 ne suka mutu inda wasu 5 suka jikkata sakamakon harin bam mayakan Houthi 'Yan Shi'a da masu goyon bayan hambararren shugaban kasar Yaman Ali Abdullah Salih suka kai a garin Ta'iz na kasar ta Yaman.

An bayyana cewa, daya daga cikin wadanda suka mutu a harin da aka nufi kasuwar Al-Shanini farar hula ne.
Haka zalika, mutane 3 da ke da alaka da sojojin gwamnatin Yaman sun mutu bayan harin bam da Houthi suka kai a wani gida da ke yankin Tibe El-Vekil.
Tsawon shekara 1 kenan garin Ta'iz ke fuskantar hare-hare daga 'yan ta'addar Houthi.
No comments:
Write Comments