Tsoro a jihar Niger yayinda wasu matsafa suka kai farmaki makarantar islamiyya sannan suka yanka yara 3
Wata mummunar kungiyar matsafa ta sanya mutane dama cikin alhini matuka bayan sun mamaye wata makarantar Islamiyya sannan kuma suka yanka yara.
Wasu matsafa dake bukatar jini sun kashe wasu yara maza guda uku da misalign karfe uku na daren ranar Laraba a wata makarantar Islamiyya dake Tungan Magajiya, karamar hukumar Rijau dake jihar Niger.
KARANTA WANNAN :- Bayan fitowa daga gidan yari, Sadik Zazzabi ya yo aman wuta (Karanta)
Da farko matsafan sun kai hari ga yara biyar ne. Biyu cikin yaran sun mutu a take yayinda dayan da akayi gaggawan kaiwa asibiti yam utu daga baya. An cire makogoron yaran sannan aka dibi jininsu a wani roba don amfani da shi, yaran da aka kashe suna tsakanin shekaru takwas da 13 a duniya.
A cewar jaridar Vanguard, daya daga cikin malamin da abun ya shafa ya tabbatar da cewa an kai hari ga yaran ne yayinda suke bacci sannan kuma aka cire masu makogwaro.
Jami’in kula da huldan jama’a na hukumar yan sandan jihar Niger, DSP Bala Elkana, ya tabbatar da al’amarin, inda yace an kai harin ne a kan maza biyar amma uku sun mutu.
Elkana ya ce: “anyi zargin cewa matsafa ne saboda sun dibi jinin yaran ne da misalign karfe 3 na safe a ranar Laraba.”
Ya bayyana cewa ana nan ana gudanar da bincike kuma cewa za’a bi sahun wadanda suka aikata laifin yayinda yace biyu daga cikin yaran sun rayu sannan yaba da tabbacin cewa za’a gurfanar da masu laifin a gaban shari’a da zaran an cefke su.
No comments:
Write Comments