
Wani babban dan kugiyar Boko Haram, Bulama
Kailani Mohammed Metele, ya mika wuya ga
rundunar sojin 145 Task Force Battalion, 5
Brigade a Damasak
Kakakin hukumar sojin Najeriya, Birgeiya Janar
Sani Usman Kukasheka ya bayyana hakan a yau
asabar a garin Maiduguri.
Janar Usman yace Metele yana bangare
Mamman Nur ne karkashin jagorancin Abu
Mustapha. Shine lamba 253 a jerin yan Boko
Haram din da ake nema ruwa a jallo.




No comments:
Write Comments