A ranar Lahadi, 4 ga watan Yuni ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu sauki sosai a lokacin da ya ziyarce shi a makon da ta gabata a London.
Tsohon gwamnan jihar Abiya, Orji Uzor Kalu
NAIJ.com ta ruwaito cewa Kalu yace shugaban kasar zai iya dawo gida
kafin ranar 11 ga wannan watan, ya kuma
bukaci 'yan Najeriya da su nisanci yada jita-jita na kiyayya game da kiwon lafiyar shugaban wanda ya ce a halin yanzu ya samu lafiya.
Yayin da yake magana a cikin wata hira a
filin jirgin sama na Murtala Muhammed da
ke Ikeja a jihar Legas, Kalu ya ce abin takaici
ne ganin yadda wasu ‘yan Najeriya ke yada
karyan jita-jita game da kiwon lafiyar
shugaba Buhari maimakon yi masa addu'a
samu domin ya koma bakin aikin sa.
Tsohon gwamnan jihar Abiya, Orji Uzor Kalu
Kalu ya ce ya ziyarci birnin Landan ne
musamma don ya duba kiwon lafiyar
shugaba Buhari.
Ya ce:
- <b>"Na tafi Washington
don na ziyarci abokan kasuwanci na kuma
daga can na biya Landan don ganin shugaban
kasa Muhammadu Buhari wanda a halin
yanzu yana murmurewa sosai.”
“Na yi farin ciki yadda na samu shugaba
Buhari duk da sakonnin kiyayya da wasu
mutane ke yadawa game da shi. Amma kuma
ina bakin ciki game da maganganu na kiyyaya
da wasu ‘yan Najeriya ke fada game da lafiyar
shugaban don na gani wa idonsu yadda
shugaban kasar yake.”</b> inji kalu
ya yabawa shugaba Buhari kan yaki da cin
hanci da rashawa kuma durkushe ‘yan
ta’adda Boko Haram.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya
bukaci mutane da su yi hakuri
No comments:
Write Comments