Hafsat Idris barauniya.
Jarumar fina-finan Kannywood Hafsa Idris, ta ce wata
shida ta kwashe tana karanta rubutaccen labarin
"Barauniya" shi ya sa ta taka rawa sosai a fim din
kamar yadda gogaggun barayi ke yi.
Hafsa, wacce ake kira 'Barauniya' ko 'Yar Fim a
Kannywood, ta shaida wa Nasidi Adamu Yahaya cewa
ta soma fim ne domin ba ta son zaman banza.
Ta kara da cewa, "Yin fim ya fi aikin gwamnati domin
kuwa abin da nake samu ma'aikacin gwamnati ba zai
samu ba."
Da fim nake yin hidimomina da na iyayena da na 'yan
uwana," in ji jarumar.
Ta kara da cewa ta koyi darasi da dama daga fim din
"Barauniya" wanda shi ne na farko da ta fara yi a
Kannywood.
Na fahimci "yadda barayi ke sata da kuma yadda satar
ke tagayyara wadanda aka yi wa".
"Na nuna jarumta da rashin tausayi da dabaru irin na
barayi," a cewar Hafsat.
"A zahiri ni ba barauniya ba ce, ba ni da son zuciya
amma da yake so ake a nuna yadda ake yin sata da
kuma irin illarta ga al'umma shi ya sa na amince na
taka wannan rawa," in ji ta.
Jarumar, wadda ta soma fim a watan Disambar 2016,
dalilin yin fim din Barauniya ya sa masu hada fina-finai
na yin ruguguwar sanya ta a fina-finansu saboda yadda
ta kware a lokaci guda.
Ta ce kowanne wata tana yin fim uku zuwa hudu
saboda "amincewar da furodusoshi" suka yi mata wajen
taka rawa a manyan fina-finai.
Jarumar ta ce tana ci gaba da "gogewa shi ya sa ma
na fito a fina-finai irin su 'Yar Fim da Rariya da
Maimunatu da Wata Ruga da sauransu."
Sai dai masu sharhi na ganin akwai jan aiki a gabanta
ganin yadda Kannywood ke cike da jarumai masu
tashe.

No comments:
Write Comments