Wednesday

Home Hhh Hhh Jakuna Da fasa kwaurin Motoci : (karanta)

Ko a wacce kasace??? biyomu





'Yan sandan Afrika ta Kudu sun dakile wani yukuri na fasakwaurin wata mota mai tsada da aka sato zuwa kasar Zimbabwe ta hanyar amfani da jakuna wajen ketarar da ita tekun Limpopo.

Mutanen da ake zargi da hannu dai sun ranci na kare zuwa cikin dajin Zimbabwe, bayan kokarin ciro motar daga turbayar da ta kafe bai yi nasara ba.

A watan Disambar bara ma an samu wata mota da aka sace a birnin Durban a gefen tekun wasu jakuna na janta.
'Yan sanda na bincike ko akwai gungun mutanen da ke da hannu a wannan sabuwar hanyar fasakauri.

Dan sanda Motlafela Mojapelo, ya ce an gano motar kirar Marsandi C220 a kusa da tekun da ba shi da nisa da Musina.
Masu fasakaurin dai sun sanya kwanon rufi a karkashin tayoyin motar ta yadda za a samu saukin curo ta daga cikin yashin da ta kafe.

Kafafen yada labaran kasar sun ambato Mista Mojapelo na cewa, "Mutanen da ake zargi da fasakaurin na amfani da jakuna wajen jan motar domin tsallaka tekun, amma jami'anmu sun isa wurin a kan lokaci suka kuma auka musu, bayan da alamu suka nuna jakunan sun kasa jan motar saboda sun gaji. "
Jakunan dai ba su ji wani rauni ba.
Ba a san dalilin da yasa masu fasa kaurin suka gwammace su yi amfani da jakuna wajen jan motar zuwa Zimbabwe ba, sai dai mai yiwuwa saboda motoci da dama na zamani ana sanya musu wata na'ura da ke amfani da tauraron dan adam wajen gano inda suke idan an sace su.
Kuma na'urar na aiki ne kawai idan ana tuka motar.

Kogin Limpopo na bakin iyakar Afrika ta Kudu da Zimbabwe kuma hanya ce da bakin haure ke amfani da ita wajen zirga-zirga tsakanin kasashen biyu.

Sai dai wakiliyar BBC a Johannesburg, Pumza Fihlani, ya ce batun cewa ana amfani da hanyar a yanzu wajen fasakaurin motoci abu ne mai ban mamaki.

Wakilin ya kara da cewa jami'an tsaro na sintiri a wurin domin hana aikata manyan lafuka.
No comments:
Write Comments