A ranar Litinin din nan gwamnatin Kenya ta tabbatar da dokar hana shigar da jakunkunan leda ko samar da su a kasar.
A ranar Litinin din nan gwamnatin Kenya ta tabbatar da dokar hana shigar da jakunkunan leda ko samar da su a kasar.
Dokar ta tanadi hukunci mai tsanani ga duk wadanda suka karya ta inda za a ci tarar dala dubu 40 ko daurin kasa da shekaru 4 ga wadanda suka saba dokar.
Kusan tsawon shekaru aka dauka kafin a tabbatar da dokar ta shafi ‘yan kasuwa, masu samar da ledar ko amfani da ita.
Ma’aikatar Kula da Mahalli ts Kenya ce ta kirkiri dokar domin magance matsalar gurbatar mahalli.
Ministan Muhalli Judy Wakhungu ya ce, jakunkunan leda barazana ce ga Kenya kuma dole ne a rabu da su.
Amma masu bincike sun bayyana cewa, sama da mutane dubu 100 ne za su rasa aiiyukansu sakamakon daukar wannan mataki.
No comments:
Write Comments