Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya tattauna ta wayar tarho da shugaban kasar Myammar Aung San Suu Çii game da halin kunci da kisan kar dangin da ake wa Musulmai a kasar.
A yayin tattaunawar shugaba Erdoğan ya ce, irin keta hakki da zaluncin da ake wa Musulman Arakan ya janyo damuwa a zukatan dukkan kasashen duniya musamman ma na Musulmi.
Shugabannin 2 sun tattauna kan batun da kuma hanyoyin da za a bi wajen kai musu kayan taimako.
Turkiyya ta la'anci harin da ake kai wa fararen hula 'yan ba ruwana, kuma tana goyon bayan dukkan wata hanya da za a bi don warware rikicin.
Erdoğan ya bukaci Myammar da ta nisanci amfani da karfi wajen murkushe Musulmai.
No comments:
Write Comments