Thursday

Home › › “Mun kashe Mataimakin Shekau ”:cewar sojin Nigeria
Rundunar sojin Najeriya ta fitar da sanarwar da ke cewa sojojinta sun kashe wasu mutane yan kungiyar Boko Haram wadanda mataimaka ne ga shugaban kungiyar Abubakar Shekau.

Sani Usman, mai magana da yawun rundunar sojin shine ya bayyana haka a ranar Talata inda yace kwamandodin kungiyar da aka kashe sune Abdu Kawuri da kuma Abubakar Benishek an kashe su ne a wani hari da sojojin suka kai a garin Alafa dake jihar Borno.
” Wannan wani kari ne akan Ba ‘Abba Ibrahim da kuma wasu kwamandodin biyu da suka mutu sakamakon raunukan da suka samu a harin kwantar baunar da sojoji suka kai musu a karamar hukumar Magumeri ta jihar Borno, ” yace.

Yace wasu manyan yan kungiyar kuma na hannun daman Shekau suma sun rasa rayukansu cikin watan Agusta bayan harin hadin gwiwa da sojoji suka kai musu.
Usman ya bayyana sabon fefan bidiyon da Shekau ya saki a matsayin wata karya da suke so suyi amfani da ita wajen jefa shakku a zukatan mutane.
No comments:
Write Comments