Kafar yada labarai ta CNN ta sanar da cewa, Amurka na shirin kai farmakai a Nijar domin daukar fansar sojojinta 4 da aka kashe a Ouallam.

A ranar Larabar nan da ta gabata, sojojin Amurka 4 da takwarorinsu na Nijar 5 sun rasa rayukansu, sakamakon wani kwantan baunar da ‘yan ta’addar Daesh suka kai musu, a kauyen Tonga-Tonga na da’irar Ouallam da ke a yammancin Jamhuriyyar Nijar.
Wannan lamarin dai ya afku ne a lokacin da sojojin na Amurka ke horar da takwarorinsu na Nijar a kan iyakar kasar da Mali.
Sanarwar da ma’aikaitar tsaron kasar Amurka Pentagon ta fitar a bayan nan, ta tabbatar da afkuwar wannan lamarin, tare da tuhumar mazaunan kauyen Tonga-Tonga, da hada baki da ‘yan haramtacciyar kungiyar DAESH.
Abinda yasa tuni a cewar tashar CNN, gwamnatin Donald Trump ta gana da shugabannin Jamhuriyyar Nijar a wajen tabbatar da aniyarsu ta kai farmakan ramuwar gayya kan dukannin wadanda ke da hannu a kisan sojojinta.
An tabbatar da cewa a yanzu haka sojojin kasar Faransa na ci gaba da bincike mai zurfi, domin tattara kwararan dalilai da kuma farautar maharan.
Source :- trt hausa.

No comments:
Write Comments