Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana a shafinsa na Twitter da cewa abu daya ne maganin Koriya ta Arewa
Trump ya kara da cewa shekaru 25 kenan muke zantawa da Koriyar amma ba'a cimma wata mafita ba, saboda haka Koriya zata girbi abinda ta shuka a cikin wadanan shekarun.
Trump ya kara da cewa Koriyar da taci gaba da karya da kuma saba yarjejeniyar da akeyi da ita nan take, abin bakin cikine yanzu mun kasance da zabi daya dilo wajen magance ta.
Kwanakin baya dai shugaba Trump ya bayyana cewa hanyar daya daya kamata abi don magance Koriya ita ce kauda ta daga doron kasa.
No comments:
Write Comments