KOWA DA IRIN NASHI: Shi Garba Dahiru, Kabari ya gina ya na kwana a ciki duk dare saboda tsoron Allah
Garba Dahiru mazaunin unguwan Yakubu Wanka ne, cikin garin Bauchi, ya ce tsananin tsoron Allah ne da zaman Kabari ya sa ya gina kabari kusa da dakinsa yake kwana kullum a ciki.
Garba ya shaida wa manema labarai haka ne a garin Bauchi da ya ke ba da bayanai akan dalilan da yasa ya maida Kabari wurin kwanansa.
Kamar yadda gidan Jaridar Aminiya ta ruwaito labarin, Garba ya ce yana haka ne domin neman gafara da tuna Mahaliccinsa.Ya ce yakan shiga ne kullum, yau Sama da shekara biyar Kenan.
” Gaskiya idan na shiga na fito ina gyara wasu laifuffukana sosai, don haka nake jin dadi sosai.
“Sannan idan na zo fita daga cikin gidana, nakan dauka idan na dawo kawai za a kawo ni cikin kabarin nan ne.
“Wannan shi ne abin da nake sanyawa a cikin raina, ina ganin kamar za a kawo ni a matsayin matacce ne, tunda Allah bai ce ga lokacin da zan mutu ba, amma dai na san kowane rai mamaci ne.
Garba ya kara da cewa yakan kuma bari ne sai dare ya yi sosai sannan ya shiga kamar karfe biyu zuwa uku sai ya shiga ya kwanta a ciki.
“Idan na shiga cikin kabarin nakan kwanta ne sai in rika surantawa a raina kamar na mutu ne ina cikin kabari. ”
Monday
Home ›
labaran abin Al'ajabi
›
Ya gina kabari ya na kwana a ciki duk dare saboda tsoron Allah : A garin Bauchi
WELCOME TO AREWASOUND

VISIT OUR NEW BLOG
- - Latest Hausa song
- - Newest Android games
- - Useful Android Apps
- - Hausa Novels
- - Health Tips
- - How to make money online 2019
AREWASOUND.COM>>> Is Your Best Solution.

Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Write Comments