Monday

Home › › An Kashe Naira Miliyan 300 Wajen Shirya Fim Din Hausa Akan Boko Haram Mai Suna ‘Make Room’

‘Make Room’ fim ne mai suna da Turanci amma aka dauke shi da harshen Hausa, sannan jaruman Kannywood kamarsu Yakubu Muhammad da Suji Jos da Sadi Sawaba da Usman Uzee da Asabe Madaki da Abba Zaky da sauransu suka taka muhimmiyar rawa a cikinsa.

Jigon labarin fim din a kan Salma (Asabe Madaki) ’yar shekara 17 ne. Salma ita kadai ce a wurin mahaifanta, kuma yarinya ce mai cike da burin yin karatun boko; yarinya ce mai jajircewa da tsayawa kai da fata wajen ganin ta cimma burinta ba tare da tunanin abin da zai je ya zo ba.

Duk burin da Salma take so ta cimma ya hadu da cikas ne a lokacin da ’yan ta’adda suka saceta hade da yin garkuwa da ita, inda ta fada cikin mawuyacin hali, sannan duniya ta yi mata daci.
Fim din ‘Make Room’ wanda kamfani Natibe Media ya dauki nauyin shirya shi, ya fito da kananan jarumai dubu uku da manya da matsakaitan jarumai 100 da kuma ma’aikatan bayan kyamara 100.

Labari ne da ke kunshe da irin yadda ’yan ta’adda suka ci karensu babu babbaka a Arewa maso Gabashin kasar nan.

An shafe fiye da kwana 50 wajen daukar fim din, inda aka dauke shi a kauyen Ijebu-Miango da ke karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato, inda aka yi hasashen kasafin kudin fim din ya kai kimanin Naira miliyan 300.

Babban Furodusan fim din, Rogers Ofime a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya ya bayyana cewa, burin da suke da shi dangane da fim din shi ne, su fafata da shi a gasar Oscar ta duniya, inda za su shiga rukuni uku da shi, wadanda suka kunshi, Gwarzon Gajeren Fim da Gwarzon Fim Ba Na Turanci Ba da kuma Gwarzuwar Jaruma, sakamakon rawar da jarumar fim din Asabe Madaki ta taka a fim din.

Ofime, wanda ya shirya manyan fina-finan Turanci irinsu ‘Oloibiri’ da ‘House of Barakat’ da kuma fitattun fina-finan Turanci da ake nunawa a gidajen talabijin irinsu ‘Tinsel’ da ‘The Johnson’ ya bayyana fim din ‘Make Room’ shi ne fim mafi wahala da ya shirya tun da ya fara harkar fim a 2001.

Ya ce, “Ba za ka taba sanin baiwa da basirarka ba sai ka samu kanka cikin wani mawuyacin halin da ba ka tunanin za ka iya fita daga cikinsa. Kafin mu kai ga daukar fim din, ina cike da burin zan shirya hadadden fim, domin ina da burin samun gudunmuwar kudi, a lokacin da muka cimma yarjejeniya da wadanda za su taimaka har rawa na yi, amma mako daya kafin mu fara daukar fim din suka janye.”
Ya ce, ya shiga cikin matsananciyar damuwa da kuma fargaba, saboda ya riga ya gayyato ma’aikata daga Amurka da Afrika ta Kudu da Najeriya da sauran wadansu kasashe.


Furodusan wanda ya lashe Gwarzon Bakon Fim a shekarar 2016 yayin Gasar Black Film Festibal da aka gudanar a San Diego, da ke Kalifoniya a Amurka, ya ce ya tambayi kansa ko ya fasa daukar fim din ne? “Sai na ce ba zan taba bari don wadanda muka yi hadaka da su sun janye in hakura ba. Domin wannan fim ne da zai yi shura a duniya.”

“Daga karshe na yanke shawarar ci gaba da daukarsa, kuma cikin ikon Allah ga shi mun kai ga karshensa.” Inji shi.
Ofime, mai kimanin shekara 44 da ya fara harkar fim da wani kamfani mai shirya fina-finai da ke Afrika ta Kudu mai suna Sky Sweeper Films a shekarar 2001, ya kara da cewa wannan fim din ya koya masa darasin komai zai yi idan zai jajirce da kuma addu’a, to zai samu nasara.


KU KARANTA A HARSHEN TURANCI


Post By ABDULLAHI H-A


No comments:
Write Comments