Tuesday

Home › › Tofa ; Gwamnonin PDP sun gabatar da sunaye 6 na 'yan takarar shugaban kasa a zaben 2019, babu sunan Atiku
Sakamakon lashe zaben ranar Asabar na
shugabancin jam'iyyar PDP da Prince Uche
Secondus yayi, rahotanni sun bayyana cewa,fatan da tsohon mataimakin shugaban kasaAtiku Abubakar na samun takarar shugabankasa a jam'iyyar ya fara samun tangarda.

A taron jam'iyyar PDP na kasa da aka
gudanar a ranar 9 ga watan Disamba,
rahotanni sun bayyana cewa wasu
gwamnonin jam'iyyar sun gabatar da
sunayen masu neman kujerar shugabancin
jam'iyyar, wanda ya nuna Uche Secondus a
matsayin shugaban jam'iyyar tun kafin a
gudanar da zaben.

Taron PDP na kasa Jaridar The Nation ta ruwaito ,wadannan gwamnoni tuni sun rigaya da tanadar sunayen 'yan takarar da
jam'iyyar za ta tsayar tun kafin sauyin sheka da Atiku yayi daga jam'iyyar APC zuwa PDP makonni biyu da suka gabata.

NAIJ.com ta ruwaito da sanadin jaridar The Nation cewa, gwamnonin sun bayar da
sunayen wadanda suke neman jam'iyyar ta
tsayar da su takara a zaben 2019 kamar
haka:

1. Tsohon gwamnan jihar Kaduna; Ahmed
Makarfi.

2. Tsohon gwamnan jihar Jigawa; Sule
Lamido.

3. Tsohon ministan ilimi; Mallam Ibrahim
Shekarau.

4. Gwamnan jihar Gombe; Ibrahim
Dankwambo.

5. Tsohon gwamnan jihar Kano; Rabi'u Musa
Kwankwaso, wanda jam'iyyar take mishi
dawo-dawo.

6. Gwamnan jihar Sokoto; Aminu Waziri
Tambuwal; wanda shima jam'iyyar take yi
mishi kiranye na dawo-dawo.
No comments:
Write Comments