Yanzu haka wani bincike da aka yi ya nuna
cewa masu amfani da harshen Hausa na
cikin wadanda su ka fi yawa a Duniya. Duk
Afrika dama dai yanzu babu yaren da yayi
fice irin na Hausa. Ana amfani da yaren a
kasashen Nahiyar barkatai.
Akwai sama da mutane miliyan 150 da ke Hausa
Spectator Index ta bayyana cewa wani nazari
da aka yi ya nuna cewa sama da mutane
miliyan 150 ke amfani da harshen na Hausa.
Yaren dai shi ne na 11 cikin sahun wadanda
su kayi fice a Duniya. Hausa na bayan irin su
harshen Mandarin ne da Hindu.
Haka zalika an tabbatar da cewa akwai masu
amfani da harshen Kasar Sifen da kuma
Larabci da yaren kasar Rasha da duk sun sha
gaban Hausa. Akwai kuma irin su Yaren
Malay da Bengali na Yankin Asiya wanda su
na gaban yaren na Hausa.
Hausa dai na bin bayan yaren Kasar Foshugal
ne da kuma Faransanci. Amma masu yaren
Hausa a Duniya sun kere yawan Jamusawa da
mutanen Fashiya da kuma masu amfani da
yaren Swahili na gida.
SOURCE : HAUSA-NAIJA.NG

No comments:
Write Comments