Nan da karshen watan gobe ne za a rufe biyan
kudin jirgi a Kasar.
Hukumar Alhazai ta Kasar nan ta raba kujeru
717 ga Jihar Kogi domin aikin hajjin bana.
Hukumar jin dadi da kula da Alhazzai na
Jihar Kogi ta bayyanawa ‘yan jarida wannan
a makon nan. Kuma Dole ne masu niyya su
tanadi takardu.
(Masu shirin sauke farali za su biya Miliyan 1.5 a bana)
Sheikh Lukman Abdullah wanda shi ne
Shugaban Hukumar Alhazzan Jihar Kogi ya
bayyanawa ‘yan jarida cewa Hukumar
NAHCON me kula da Mahajjatan Najeriya ta
rage yawan kujerun da ta saba ba Jihar Kogi
a bana.
Abdullah yake cewa a wannan shekarar, an
warewa Jihar Kogi kujeru 717 ne yayin da a
bara kuwa an ba Jihar kujeru sama da 830.
Sheikh Abdullahi ya bayyana wannan ne
lokacin da yake zantawa da manema labarai
a Garin Lokoja.
A cewar Shugaban Hukumar Alhazzan na
Jihar, lokaci ne zai kawo masu cikas wajen
shiryawa aikin na Hajjin bana. An dai bada
nan da karshen watan uku a kamalla biyan
kudin sauke faralin wanda yanzu ya kai
Naira Miliyan daya da rabi.

No comments:
Write Comments