Wednesday

Home Inaso Kwankwaso Ya Dawo PDP : Cewar Tsohon Gwamana Shekarau.

Tsohon Gwmanan jihar Kano kuma jigo a jam'iyyar PDP Malam Ibrahim Shekarau ya ce zai yi farin ciki idan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya koma PDP daga jam'iyyar APC. Ana rade-radin cewa jagoran na Kwankwasiyya zai iya barin jam'iyyar APC bayan da uwar jam'iyyar ta goyi bayan Gwamna Abdullahi Ganduje a rikicin shugabancin da suke yi.
Hakazalika kuma ana ganin yana sha'awar yin takarar shugabancin kasar a zaben 2019, sai dai bai fito ya bayyana hakan ba kawo yanzu. Sai dai Malam Shekarau, wanda shi ma ke son yin takarar shugabancin kasar a PDP, ya shaida wa BBC cewa kawo yanzu babu wata magana tsakaninsa da Kwankwaso kan shirin komawarsa PDP. An dade ana rashin jituwa a siyasance tsakanin Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wadanda duka manyan 'yan siyasa ne a Najeriya. Ya ce ko a baya ma, ba shi da wata matsala tsakaninsa da Kwankwaso, kuma ba shigar Kwankwaso APC ce ta sa ya fita ba. Duka mutanen biyu sun mulki jihar Kano tsawon shekara takwas-takwas, kuma suna da dimbin magoya baya. Kuma wasu na ganin hadewarsu wuri guda za ta bai wa jam'iyyar APC gagarumar matsala ba wai a Kano ba nhar ma da wasu sassan kasar. SOURCE AT BBCHAUSA
No comments:
Write Comments