Al'ummar garin Bitiah Irruan dake a
karamar hukumar Boki ta jihar Kuros
Ribas sun shiga rudani biyo bayan wani
gwaggwan biri da ya biyo wani manomin
kauyen har gida bayan ya dawo daga gona
a ranar Juma'ar da ta gabata.
Kamar dai yadda muka samu, wani
ma'abocin anfani da kafar sadarwar
zamani ta Facebook mai suna Osang
Gabriel ne ya shelanta hakan a shafin
sa inda kuma ya bayyana cewa hakan
ya ja hankalin al'ummar kauyen sosai
da ma makwafta.
NAIJ.com ta samu cewa yanzu haka dai
komai ya fara lafawa a kauyen amma
labarin na cigaba da yaduwa tare kuma
da daukar hankali a sassa daban daban
a fadin kasar nan.
No comments:
Write Comments