Saturday

Home Yanzu Yanzu: Kotu ta yanke wa Ronaldo hukuncin zaman gidan yari

Wata kotun kasar Andalus ta yanke wa fittacen dan kwalon Real Madrid, Cristiano Ronaldo hukuncin zaman gidan yari na shekaru biyu saboda kauracewa biyan haraji da gangan. Sai dai an ruwaito cewa Ronaldo ya nemi sassauci inda ya ke bukatar a janye hukuncin zuwa gidan yarin don ya biyaya kudaden da binsa tare da warware matsalar baki daya kamar yadda muka samo daga jaridar Daily Trust.
Lauyoyin kasar Andalus ne suka zargi Ronaldo da laifin kaucewa biyan haraji a watan Yunin shekarar 2017 inda suka ce kudadedn harajin da ya kamata ya biya gwamnati sun kai £12.9 miliyan. Ronaldo ya musanta zargin kauracewa biyan harajin a wancan lokacin da ya gurfana gaban kotu sai dai ba'a kammala shari'ar ba. Da farko dai gwamnati ta ki amincewa da kudin da ya biya a watan Mayu sai dai jaridar El Mundo ta yi ikirarin cewa ya amince da hukuncin zuwa gidan yari tare da amsa laifinsa don sassauta masa kudin da zai biya. Zai kuma biya zunzurutun kudi har £16.4 miliyan kuma tunda ba'a taba samun Ronaldo da wani laifi a baya ba, ba zai je gidan yari ba. Da farko dai an bukaci Ronaldo ya biyya dukkan kudaden da ake zarginsa da kin biya gaba daya sai dai daga bisani an cinma matsaya inda aka umurci ya biya £5 miliyan kawai. Sai dai a halin yanzu bai riga ya rattaba hannu kan yarjejeniyar ba amma mudin ya sa hannu, za'a kawo karshen wannan shari'a da ake dade ana yi. Ronaldo zai kasance tare da sauran yan wasan kasar Andalus a gasar cin kofin duniya da kara da Portugal a daren Juma'a.
No comments:
Write Comments