Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin Zonal Chairman din kungiyar, Dr Ade Adejumo yayin wata hira da ya yi da manema labarai a Ibadan inda ya ce tawagar gwamnatin tarayya karkashin kagorancin Dr Wale Babalakin ne suka sanar dashi yayin da suka ziyarci kungiyar a Ibadan.
Ya yi kira da 'yan Najeriya su hada karfi da karfe da kungiyar domin ganin cewa gwamnatin ta dauki matakan habbaka karatu a jami'o'in gwamnati.
Kungiyar kuma tayi kira ga gwamnatin tarayya ta cika mata alkawurran da suke cikin yarjejeniyar da ASUU da gwamnati suka rattaba hannu a shekarar 2017 idan kuma ba hakan ba akwai yiwuwar kungiyar ta shiga yajin aiki.
Kazalika, kungiyar ta ce babu kanshin gaskiya cikin ikirarin da gwamnati tayi na cewa ta bawa kungiyar N20 biliyan domin a cewarsu makarantu aka bawa kudaden ba kungiyar ASUU ba. Ta ce abin dariya ne gwamnatin tayi alfahari da bawa jami'o'i 64 N20 biliyan domin ya yi kadan.
No comments:
Write Comments