Akwai sauran aiki kafin Gwamnatin Buhari ta kara albashin Ma’aikata Fadar Shugaban kasa ta ce ana yi wa jawabin da Shugaban kasa Buhari yayi wajen karbar rahoton karin albashin Ma’aikatan Najeriya daga hannun shugaban kwamitin da aka nada Ama Peple wani irin fassaran da bai dace ba.
Wata Majiya daga fadara Shugaban kasar tace Shugaba Muhammadu Buhari bai bayyana cewa yayi amanna da wannan mataki da kwamiti ta dauka na kara albashi ba, illa iyaka dai ya yabawa aikin da kwamitin tayi ne kurum.
Wani da ya ki bari a bayyana sunan sa a cikin fadar Shugaban kasar ya bayyanawa menama labarai wannan. Wannan Bawan Allah yace ana ta azarbabin rahoto cewa Shugaba Buhari ya kara albashi nan take wanda sam ba haka bane.
A cewar wannan mutumi, dole sai an mikawa Majalisar zartarwa na Gwamnatin Tarayya watau FEC da kuma Majalisar da ke aiki kan tattalin arzikin Najeriya na NEC domin duba aikin da wannan kwamiti tayi kafin a je ko ina a Gwamnati. Haka-zalika mun kuma samu labari cewa sai an aikawa Majalisar Tarayya kudirin game da karin albashin kafin Gwamnati ta soma biyan Ma’aikatan kasar sabon albashi.
Majiyar tace ba Shugaban kasa bane kurum ke da iko a lamarin.
SOURCE HAUSALEGIT.NG

No comments:
Write Comments