Kungiyar CNPP da ke rike da lemar Jam’iyyun
Najeriya sun hurowa Shugaban kasa Buhari
wuta ya binciki zargin da ake yi wa Gwamnan
Jihar Kano na karbar rashawar Daloli daga
hannun ‘Yan kwangila idan har da gaske ana yi
yakar barayi a Kasar.
Jam’iyyun siyasar Kasar nan sun ba Hukumar
EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin
kasa wa’adin makonni 2 su fara binciken
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje. Sakataren
Kungiyar ta CNPP, Willy Ezugwu ne yayi wannan
bayani a makon nan.
Sakataren na CNPP ya bayyana cewa su na
zargin Gwamnatin Shugaban kasa Buhari da
Hukumar EFCC da ke karkashin shugabancin
Ibrahim Magu tana nuna son kai wajen yakar
barayin Najeriya. CNPP tace ya kamata EFCC tayi abin da ya dace.
Willy Ezugwu ya soki yadda Kotu ta sa a dakatar
da binciken da ake yi kan Gwamnan na Kano
inda tace Hukumar EFCC ta zama karen farautar
Shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ‘Yan
siyasan APC su ke cin karen su babu babbaka a
Najeriya.
Kungiyar ta CNPP ta kuma yi tir da yadda
Gwamna Abdullahi Ganduje ya ki halartar
zaman da Majalisar dokokin Jihar ta gudanar da
kwanaki. Ezugwu ya kuma yi Allah-wadai da
yadda Shugaban kasa Buhari yayi mursisi game
da badakalar.
SOURCE:LEGITHAUSA.NG
No comments:
Write Comments