Thursday

Home Yanzu-Yanzu - Hukumar INEC na ganawar sirri don sake duba zaben shugaban kasa
Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) na cikin wata ganawa domin sake duba zaben Shugaban kasa da na yan majalisa da ya gudana a ranar Asabar da ya gabata.

Ganawar wanda ke zuwa yan sa’o’i bayan zaben na gudana ne tsakanin tawagar hukumar INEC da kwamishinonin zabe.



A jawabin bude taro, Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa za a sake duba ga tsarin da kuma matakan da aka bi sannan ayi gyara inda bukatar hakan ta taso.

Ya kuma bayyana cewa ganawar zai taimaka wajen kammala tsare-tsare na zaben gwamnoni da ke zuwa a jihohi 29 na tarayyar kasar da kuma zaben kwamiti na birnin tarayya.

A baya mun ji cewa Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta lashe kujeru mafi rinjaye a sabuwar majalisar dattawan da za'a shiga inda ta samu kujeru akalla 64 a zaben da ya gudana ranar Asabar, 23 ga watan Febrairu, 2019.

DUBA WANNAN : Dabban Dalilin da Yasa Ban taya Buhari Murna ba : Cewar Atiku,

Jam'iyyar adawa da Peoples Democratic Party (PDP) ta samu kujeru 40, jam'iyyar YPP ta samu kujera daya kacal, yayinda sauraron sakamakon kujeru 2 daga jihar Plateau, 1 daga jihar Taraba, da daya daga jihar Imo.
No comments:
Write Comments